Kakaki da ‘yan majalisa 12 sun koma APC daga PDP a Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon. Bilyaminu Moriki, da wasu mambobin majalisar 12 sun bar jam’iyyar adawa ta PDP tare da koma wa mai mulki, APC.

Hon. Moriki ya sanar da haka yayin zaman majalisar a jiya Litinin a Gusau bayan gabatar da takardun murabus ɗinsu ga majalisar.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito cewa matakin ‘yan majalisar ya biyo bayan sauya sheƙar gwamnan jihar, Dauda Lawal ne daga PDP zuwa APC.

A yau Talata ne ake sa ran karɓar gwamnan a APC a hukumance, kamar yadda Sakatariyar jam’iyyar ta Ƙasa ta bayyana.

Taron zai ƙunshi Maitaimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da jagororin APC da kuma tsofaffin gwamnonin jihar.

Haka kuma za a tarbi ‘yan majalisar da suka sauya sheƙar a hukumance tare da gwamnan.

Daga cikin waɗanda suka koma APCn akwai mataimakin kakakin majalisar Adamu Aliyu (mazaɓar Gummi II); Jagoran mafiya rinjaye, Bello Mazawaje (mazaɓar Tsafe ta Gabas), da Mai tsawatarwa, Rilwanu Nagambo (mazaɓar Anka), da dai sauransu.

Wannan mataki ya nuna cewa a yanzu APC ta karɓe jagorancin majalisar, inda baki ɗaya ‘yan majalisar 24 suka koma cikinta.

By Babaji