Zamfara: An gargaɗi matasan APC kada su ɗauki makami wajen tarben Kashim Shetima

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

An yi Kira ga mambobin jam’iyyar APC musamman matasa da su guji ɗaukar duk wani irin makami a wajen tarbon mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shetima da zai zo jihar don karɓar Gwamna Dauda Lawal zuwa jam’iyyar ta APC a gobe Talata.

Shugaban kwamitin yaɗa labarai na tarbon mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shatima, Hon. Lawal M. Liman yayi wannan kira a lokacin da kwamitin ke ganawa da manema labarai a Gidan Gwamnatin Jihar cikin daren nan.

A cewar sa, an kammala duk shirye shiryen taron mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shatima, yana mai nuni da cewar baza a amince da amfani da duk wani yunƙurin kawo matsala a lokacin ziyarar mataimakin Shugaban ƙasar ba.

Ya ƙara da cewar kwamitin su zai sanya ido sosai don ganin an kammala taron cikin nasara da lumana.

Hakazalika Hon. M. Liman yayi Kira ga mambobin jam’iyyar da magoya bayan ta a Jihar da su fito don tarbon mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shatima.

Ya kuma yi kira gare su da su kasance masu bin doka da oda don tabbatar da an kammala taron cikin kwanciyar hankali.

By ukarofi