Kakakin KAFIGAN, Al-Amin Ciroma ya yi murabus

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Daraktan yaɗa labarai kuma mamban kwamitin amintattu (BOT) na ƙungiyar masu shirya fina-finai ta KAFIGAN, Al-Amin Ciroma ya yi murabus daga muƙaminsa.

A wata takarda da ya aike wa Darakta Janar na ƙungiyar, Ciroma ya ce ɗauki matakin ne duk da cewa yana da muhimmiyar rawa da yake takawa wajen tafiyar da harkokin ƙungiyar.

Ya ce, lokaci ya yi da ya dace ya ajiye aikin sakamakon wasu dalilai na raɗin kansa.

Ya kuma yi godiya ga hukumar gudanarwar ƙungiyar bisa damar da ta ba shi na gagarumim matsayin wanda ya yi amfani da ƙwarewa da sadaukarwarsa a kai.

Ciroma ya ƙara da cewa, ya fahimci duk yadda mutum ke ƙoƙarin wajen bada gudumuwa a matsayin da aka ɗora masa, to akwai yiwuwar wani lokaci a cigaba da tafiya ba tare da shi a wajen ba sakamakon waɗansu dalilai.

Kazalika, ya yi wa KAFIGAN addu’o’i da fatan alkhairi a al’amuranta a yanzu da nan gaba gami da fatan samun haɗin kai mai ɗorewa a tsakanin mambobinta.

By Babaji