Kalaman Trump sun ƙara ƙarfin ƙungiyoyin ta’addanci a Nijeriya – Akume

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta ce, sabbin hare-haren da ‘yan ta’adda da barayin daji suka ƙaddamar cikin kwanakin nan a sassan Nijeriya sun samo asali ne daga kalaman da shugaban Amurka Donald Trump ya yi kwanan nan game da Nijeriya.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta yi tsokaci kan yadda ƙungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi da ɓarayin daji ke sake farfaɗowa a faɗin ƙasar.

Ya ce, kalaman shugaban Amurka sun ba wa wasu rukunan ta’addanci damar neman tagomashi da janyo hankalin duniya ta hanyar kai hare-hare kan wuraren da ba su da tsaro.

A watan Oktoba, Trump ya shelanta cewa Nijeriya tana fama da abin da ya kira “kisan Kirsitoci”, tare da barazanar katse duk wani tallafi na Amurka ga Nijeriya.

Haka kuma ya yi barazanar tura sojojin Amurka ƙasar idan gwamnatin tarayya ta kasa magance zarge-zargen da ake yi. Trump ya kuma umurci Ma’aikatar Yaƙi ta Amurka ta fara shirin “yiwuwar ɗaukar mataki” idan tashin hankalin ya ci gaba.

Akume ya ce, kafin waɗannan kalamai, an riga an rage ƙarfin ƙungiyoyin ta’addanci a Nijeriya, inda suka koma ƙananan hare-haren fasa-ƙundu da kwace shanu. Amma bayan kalaman Trump, wasu ƙungiyoyi suka fara ƙoƙarin amfani da wannan yanayi domin su sami suna da ƙarin tallafi daga ƙasashen waje.

Ya ce, “Kafin waɗannan maganganu daga Amurka, an riga an ragargaza tsarin ƙungiyoyin ta’addanci, suka koma abin da ya kama da ɗan fashi-fashi. Wannan dawowar tashin hankali ya nuna buƙatar haɗin kai, ba wai yi wa ƙasa laƙabi daga waje ba.”

Akume ya kuma jaddada cewa Nijeriya ba ta buƙatar sojojin ƙasashen waje don maido da zaman lafiya. A cewarsa, rundunar soja ta ƙasar nan ta sha gogewa, tana da ƙarfi, kuma ta riga ta kwato yawancin yankunan da Boko Haram da ISWAP suka mamaye a baya.

Sai dai ya yarda cewa, duk da irin nasarorin da aka samu, Nijeriya na buƙatar taimako daga ƙasashen waje — musamman wajen bayanan leƙen asiri, fasahar zamani da kayan aiki masu ƙarfi – domin ƙarfafa yakar ta’addanci.

Akume ya yi watsi da iƙirarin cewa ana kashe Kirsitoci kawai a Nijeriya. Ya ce bincike ya nuna cewa ‘yan ta’adda suna kai hari ga masallatai da coci-coci, suna hallaka Musulmai da Kiristoci ba bambanci ba.

A cewarsa, Nijeriya ƙasa ce mai bin tsarin dimokuraɗiyya kuma babu wani addini da aka ɗora a matsayin addinin ƙasa. Ya ce naɗe-naɗen gwamnati na gudanarwa sun nuna bambancin al’ummomin Nijeriya ba tare da fifikon addini ko ƙabila ba.

Sai dai hare-haren ta’addanci sun ƙaru cikin ‘yan makonnin nan, ciki har da kisan wani jami’in soja, sace ɗalibai mata, da kuma harin da aka kai wani coci a jihar Kwara wanda ya ƙara haifar da fargaba a tsakanin jama’a.

By ukarofi