Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsofaffin mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano sun ƙaryata wani rahoton da ya yaɗu a kafofin watsa labarai da ke cewa sun amince da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben 2027.
Yayin da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan ɓullar rahoton da suka kira na bogi, ɗaya daga cikin tsofaffin ‘yan majalisar — wanda ya nemi a ɓoye sunansa — ya ce labarin ba shi da tushe, kuma ba shi da alaƙa da abin da ya kai su wurin taron da suka yi da Sanata Barau.
A cewarsa, “Sanata Barau kawai ya gayyace mu ne domin wani taro. A matsayinsa na babban jigo a APC, mun ga ya dace mu girmama gayyatar. Mun tattauna batutuwa da dama kan ci gaban jam’iyya, amma babu wani lokaci da muka tsayar da shi a matsayin ɗan takara.”
Ya ce, sun firgita matuƙa ganin yadda aka ƙirƙiri labarin da ya zargi taron da cewa sun mara wa Barau baya a zaɓen 2027. Ya bayyana shi a matsayin ƙarya tsagwaronta.
Wani tsohon ɗan majalisa da ya halarci taron shi ma ya yi allah-wadai da rahoton, yana mai cewa “labarin da ake yaɗawa ya raina hankali ne. Ba mu tattauna batun tsayar da kowa ba. Abin da ya kawo mu shi ne haɗa kan jam’iyya da ƙarfafa APC gabanin 2027.”
Ya ce, wasu mutane na ƙoƙarin hura wutar rikici ta hanyar yaɗa abubuwan da ba su faru ba, duk da cewa APC na da tsari mai bayyana yadda ake fitar da ɗan takara.
“Na shiga taron ne saboda mutunci da nauyin jam’iyya, ba don tallafa wa wani ba. Mutane su daina karkatar da bayanai don son rai,” inji shi.
Ya bayyana cewa har ma rahoton ya jawo ɗan tashin hankali tsakaninsu, abin da ya sa suka kira wani taro na gaggawa domin fayyace batun, su kawar da duk wani ruɗani.
Ya ƙara da cewa, ba a yi wa Sanata Barau ko wani ɗan takara wani nau’in goyon baya ba, domin APC na da masu sha’awar takara da dama, kuma kowa na san jam’iyyar na da tsarin ta na fidda ɗan takara.
“A matsayinmu na manyan ‘yan jam’iyya, za mu iya halartar kiran duk wani ɗan takara da ya nemi ganawa da mu. Amma tsarin jam’iyya ne zai fitar da wanda zai tsaya, sannan mu ba shi cikakken goyon baya,” inji shi.
A ƙarshe, tsofaffin ‘yan majalisar sun roƙi jama’a da magoya bayan APC su yi watsi da rahoton da ya yaɗu, suna mai cewa labarin ƙage ne, babu wata gaskiya a cikinsa.
