Gwamnati ta rufe makarantun sakandire a Jihar Filato

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI, Jos

Gwamnatin Jihar Filato ta ƙarƙashin Hukumar Kula Da Ilimin Ƙananan Makarantu ta Bai ɗaya (SUBEB), ta fitar da sanarwar rufe dukkan ƙananan makarantun sakandire da ke faɗin jihar, a wani ɓangare na ɗaukar matakin rigakafi don kare ɗaliban jihar daga faɗawa hannun ƴan bindiga da ke satar ƴan makaranta a jihohin Arewa.

Sanarwar ta cigaba da cewa, gwamnati ta yanke shawarar ɗaukar matakin ne sakamakon wata buƙatar gaggawa da ta taso. Sai dai ta ce, wannan mataki ne na wucin gadi ba abu ne da zai jima ba.

Rufe makarantun zai fara ne daga ƙananan makarantun sakandire na Gwamnati da ake kira da Government Junior Model Secondary Schools (GJMSS), wanda zai fara daga ranar Asabar 22 ga watan Nuwamba, 2025. Sannan sauran makarantun firamare da sakandire na gwamnati su ma a rufe su daga ranar Litinin 24 ga watan Nuwamba, 2025.

Don haka SUBEB ta yi kira ga dukkan hukumomin da ke kula da ilimi a ƙananan hukumomin Jihar Filato 17 su yi biyayya ga wannan umarni.

Tuni dama iyaye da wasu mazauna jihar suka yi ta kiraye-kiraye ga gwamnati da a gaggauta rufe makarantun, saboda ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a ɓangaren ilimi, musamman kasancewar jihar na cikin jihohin da ke fuskantar hare-haren ƴan ta’adda a yankin ƙananan hukumomin Wase, Kanam, Bokkos, Riyom, Bassa, da Barikin Ladi.

By ukarofi