
Gwamnatin Tarayya ta sanar da haramta bai wa dukkan wani jami’in gwamnati mai riƙe da muƙami digirin girmamawa a ƙoƙarinta na daƙile yawan saɓa wa ƙa’ida wajen bayar da irin shaidar.
Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ce ta bayyana hakan, inda ta ce ta ɗauki matakin ne bayan samun rahotanni masu tayar da hankali game da yadda ake bayar da digirin girmamawa barkatai da amfani da su ta hanyoyin da ba su dace ba.
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Yusufu Ribadu ne ya bayyana hakan a Abuja, jim kadan bayan karbar rahoton kwamitin bincike kan yadda ake bayarwa da amfani da digirin girmamawa a faɗin ƙasar.
A cewarsa, binciken da NUC ta gudanar ya gano yadda ake ta’ammali da digirin girmamawa ba bisa ka’ida ba, musamman karya dokokin Keffi Declaration na shekara ta 2012, wadda ta tanadi cewa jami’o’i ba su da hurumin ba wa masu rike da mukaman gwamnati irin waɗannan digirgir.
Ya ce, dokar ta kuma haramta wa duk mai karbar digirin girmamawa amfani da lakabin “Dr” sai dai a bayyana shi da sunan da ya dace, kamar Doctor of Literature (Honoris Causa).
Farfesa Ribaɗu ya bayyana cewa wannan ba kawai batun ladabi ko tsarin aiki ba ne, saidai abu ne da ke da nasaba da dokoki, domin amfani da laƙabin ‘Dr’ ba tare da cikakken bayani ba na iya zama laifi a ƙarƙashin dokokin da suka shafi yaudara a Nijeriya.
