Daga BASHIR ISAH
Kamfanin buga jaridun Blueprint da Manhaja ya yi rashin ma’aikaci mai suna Malam Ado Musa wanda aka fi sani da Fancy.
Marigayi Musa na aiki da kamfanin Blueprint ne a ofishinsa na shiyyar Kano da ke Tabloid.
Ya rasu ne sakamakon fama da rashin lafiya, inda ya bar mahaifinsa da mata biyu da kuma ‘ya’ya 12.
Kafin rasuwarsa, marigayin shi ne mai kula da rarraba jaridun Blueprint a ofishin kamfanin na Kano wanda ya ba da gudunmawarsa matuƙa wajen tabbatar da jaridun na karaɗe sassan jihar Kano.
Mahaifin marigayin ya bayyana ɗansa a matsayin mai ƙwazo wanda ilahirin ahalin gidan za su yi rashinsa matuƙa.
A nasa ɓagare, Babban Jami’i mai kula da ofishin Jaridun Blueprint a Kano, Malam Bashir Mohammed, ya bayyana Musa a matsayin mutum mai aiki da gaskiya da kuma iya jure ma kowane irin ƙalubale a bakin aiki.
Haka shi ma Jami’i mai kula da ɓangaren tallace-tallace na Blueprint a Kano, Malam Kaniru Fumtua, ya ce a halin rayuwarsa, marigayin ya kasance mai biyayya wanda ba ya wasa da aikinsa.
Tuni dai aka yi jana’izar marigayin daidai da karantarwar addinin Musulunci.