Kamfanin KAEDCO zai iya rasa lasisinsa sakamakon Bashin Naira biliyan 51.93

Daga AMINA YUSUF ALI

Kamfanin rarraba wutar lantarki na jihar Kaduna (KAEDCO) yana fuskantar barazanar rasa lasisin gudanar da kamfanonin saboda bashin Naira biliyan 51.93.

Kamfanin KAEDCO ya amshi sanarwa daga hukumar kula da ƙa’idojin wutar Lantarki (NERC) a ranar Litinin xin da ta gabata. Inda ake umartar Bankin game da niyyar NERC na soke lasisinsa na gudanarwa.

Wasu rahotanni da suka bayyana a ranar Talatar da ta gabata sun bayyana cewa, KAEDCO ta tara wa kanta bashin Naira biliyan 41.49 a tsakanin shekaru 2015 zuwa 2021, wanda Hukumar rarraba wutar ta Nijeriya a kan sari (NBET) da MO suka biyo shi.

A shekarar 2022, kamfanin wutar na Kaduna (Disco), ya ƙara tara bashin har na Naira 51.93 daga NBET da MO, abinda idan aka haɗa ya zama jimillar Naira 93.41 daga 2015 zuwa 2022.

NERC ya bayyana cewa, yana da ƙwaƙƙwarar hujjar cewa, KAEDCO ya sava ma tanade-tanaden dokar sashen wutar lantarki (EPSRA) da kuma sharuɗɗa da dokokin lasisin rarraba wutar lantarki.

A halin da ake ciki dai, NERC ta ba wa Kamfanin Disco na Kaduna kwanaki 60 domin ta sasanta maganar bashin nan ko ta fuskanci soke lasisinta.

Wannan al’amari ya zo ne bayan makwanni da dama da kamfanin (TCN) ya yanke KAEDCO daga wutar Nijeriya gabaɗaya, kafin daga bisani kuma a sake dawowa a jona ta.