Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban kamfanin Alhaji Aƙilu Hassan Mohammed ya sanar da haka a Katsina lokacin da yake hira da manema labarai.
Ya ce an kammala duk shirye shirye domin kamfanin ya fara aikin mulmula ƙarafan.
Alhaji Aƙilu ya sanar da ɗaukan ma’aikata 1000 da zasu fara aiki a sassan kamfanin da kuma ƙarin wasu ƙwararru da za a ɗauka nan bada jimawa.
Ya bayyana cewa sun tanadi isassun kuɗaɗe na gyaran gine gine da na’urori na mulmula ƙarafa domin maido da su aiki gadan gadan.
“Da zarar kamfanin ya fara aiki zai taimaka wajen samar da aikin yi da bunƙasa tattalin arzikin Jihar Katsina da ma Arewacin ƙasan,”inji shugaban kamfanin.
Ya kuma sanar da cewa kamfanin ya ɗauko ƙwararru yan ƙasan waje da za su taimaka wajen bada horo ga ma’aikatan kamfanin.
“Kamfanin zai biya haraji da duk wasu abinda ya dace ga gwamnatin Jihar Katsina”inji Aƙilu. Sai yayi kira ga gwamnatin Jihar Katsina da ta cigaba da basu goyon baya domin ganin samun nasarar wannan shiri.
Kamfanin mulmula ƙarafa na Katsina da aka gina fiye da shekaru arba’in da suka wuce, tsohon shugaban ƙasa marigayi Alhaji Shehu Shagari ya ƙaddamar da ɓuɗewa.
Sai dai kamfanin ya sha samun matsaloli na mallaka tsakanin gwamnatin tarayya da kamfanoni masu zaman kan su kafin wannan Kamfanin NAK na ƴan ƙasa ya mallaka.
