Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina ya yi wannan magana ne a garin Dutsinma lokacin da yake ƙaddamar da rabon kayan abinci ga waɗannan hare haren ƴan bindiga ya shafa wanda ƙungiyar cigaban Dutsinma ta samar.
Ya ce shi abinda ke a gaban sa shine gudanar da ayyukan cigaba a jihar da shugabanci na gaskiya da tsoron Allah.
“Naga hotuna na da wasu takardu na yawo da yake nuna ina neman kujerar mataimakin shugaban ƙasa wanda hakan ba gaskiya bane, ni dai abinda na sa a gaba shine gudanar da ayyukan cigaba a jihar wanda dalilin haka yasa al’ummar jihar suka zaɓe ni.”Inji malam Dikko.
“Bani da hannu wajen kamfen da wasu ke yi na neman nayi takarar kujerar mataimakin shugaban ƙasa, abinda na sa a gaba shine sauke nauyin da al’ummar Jihar Katsina suka ɗora mani kuma shi nake yi.”Raɗɗa ya ce .
Gwamna Raɗɗa ya kuma yabawa Ƙungiyar cigaban Dutsinma da ta bada wannan tallafi ga waɗanda hare haren ƴan bindiga a shafa.
“Wannan abun alheri da kukayi ya nuna yadda kuke ƙaunar juna da taimakawa juna a tsakanin ku.”inji Dikko Raɗɗa.
Ya kuma yabawa Hon Aminu Balele ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Dutsinma da Kurfi da ya bada taimakon Naira miliyan shida a matsayin nasa gudunmawar.
Dikko Raɗɗa ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na samar da tsaro a jihar wanda a cewar sa shine ta sa a gaba.
Ya ce gwamnatin sa na aiki ba dare ba rana wajen kawo zaman lafiya a jihar.
Ƙungiyar ta raba buhun masara guda 600 da Naira 5000 ga kowane mutum da hare haren ƴan bindiga ya shafa a yankin.
