
Daga BELLO A. BABAJI
Darakta Manaja na Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN), Ali M. Ali ya ce kamfanin ya na bin tsarin sabuwar fasaha ta AI wajen gudanar da harkokinsa, lamarin da ya inganta ayyukansu wajen tsare gaskiya da adalci gami da amfani da ƙwarewa daidai da zamani.
Ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa na martaba ranar aikin jarida ta duniya ta shekarar 2025, ranar Asabar.
Majalisar Harkokin yaɗa labarai ta Ƙasa, NPC, ta shirya taron a Abuja don tattauna yadda fasahar AI ta inganta harkokin aikin jarida a Nijeriya.
Shugaban kamfanin ya ce, gidajen jaridu suna da haƙƙin samar da shirye-shiryen da za su inganta kowane fannin ci-gaba a Nijeriya ta hanyar amfani da fasahar.
Haka kuma ce, lallai fasahar ta kawo sauyi mai alfano gami da yin kyakkyawan tsari, wanda ya taimaka wa kamfanin wajen fitar da labarai cikin ƙanƙanin lokaci.
Lamarin da ya sa ake iya fitar da labarai cikin harshen Hausa a sauƙaƙe, inda ya ce nan ba da jimawa ba za su fara fitarwa ta wasu yaruka.
