Daga MUHAMMAD AL-AMIN, Damaturu
A wani sabon harin da ake zargin mayaƙan Boko Haram da aiwatar dashi a sansanin sojojin Nijeriya, na bataliya ta 27 dake garin Buni -Yadi, a ƙaramar hukumar Gujba, ta jihar Yobe, ya yi sanadiyar mutuwar sojojin huɗu tare da lalata makamai a cikin harin.
Wani ganau, wanda ya tsallake rijiya da baya a harin, ya shaida wa MANHAJA cewa maharan sun kai farmakin da kimanin ƙarfe 2:00 na tsakiyar daren Jummu’a; wayewar safiyar Asabar.
“Yayin da kuma maharan suka fara da tarwatsa wani abin fashewa, wanda ƙarar harbe-harben bindigogi masu aman wuta ya biyo baya, amma duk da haka ba mu yi ƙasa a gwiwa ba, wajen mayar da martani. Amma sun lalata makamai da sauran motocin da muke amfani dasu.”
“Cikin alhini, mun rasa sojoji huɗu, kamar yadda su ma basu sha da daɗi ba, inda su ma sun yi asarar rayukan mayaƙan su, a cikin wannan gumurzu wanda ya ɗauki sa’o’i ana bata-kashi.” Ya bayyana.
A hannu guda kuma, ita ma hedikwatar sojojin Nijeriya, ta tabbatar da cewa an kai harin, a shafinta na Facebook a safiyar Asabar.
Sanarwar ta bayyana cewa, “Sojojin rundunar HAƊIN KAI sun mayar da martani mai tsanani a lokacin da mayaƙan ISWAP suka kai musu hari a Buni Yadi, dake Jihar Yobe. Amma cikakkun bayanai za su zo daga baya.”
Buni Yadi na da tazarar nisan kilomita 65 daga Damaturu, babban birnin jihar, kuma nan ne mahaifar Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni.
Wannan sabon harin ya na zuwa ne ƙasa ga awanni 24 bayan da kungiyar gwamnonin Arewa maso Gabas, suka gudanar da taro, a Damaturu, yayin da gamayyar gwamnonin suka buƙaci gwamnatin tarayya ta matsa ƙaimi wajen magance matsalolin tsaro a yankin.
