Daga USMAN KAROFI
Hukumar ICPC ta bayyana cewa ta yi kuskure a sanarwar da ta fitar, inda ta zargi hukumar bayar da lamunin ɗalibai ta Najeriya (NELFUND) da almundahana da kuskuren bayanan kuɗi. A baya, ICPC ta ce an rasa bayanan kashe Naira biliyan 71 daga cikin Naira biliyan 100 da aka ware don bayar da rancen, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen yaɗa labarai.
Sai dai hukumar NELFUND ta ƙaryata wannan zargi, tana mai cewa rahoton na ICPC “ƙarya ne, kuma ya zama abin kunya ga shirin.” Daga bisani, ICPC ta sake fitar da wata sanarwa inda ta amsa cewa ta yi kuskure, tana mai bayanin cewa bincikenta ba ya kan NELFUND kai tsaye, sai dai akan jami’o’i da ake zargi da ƙin isar da kuɗin da aka tura musu.
Shugaban ICPC, Musa Adamu Aliyu, ya shaida wa BBC Hausa cewa kuɗin da NELFUND ke bayarwa yana zuwa ne kai tsaye ga asusun makarantu da ɗalibai, amma ɗaliban na ƙorafi cewa wasu makarantu ba su amsa kuɗin ba ko kuma suna caji fiye da yadda ya dace. Ya ce babu wasu kudi da aka rasa daga asusun rancen, kuma kuskuren da aka yi ya samo asali ne daga fahimtar da ba ta dace ba.
