




Daga BELLO A. BABAJI
A wani yunƙuri na nuna goyon bayan ci-gaban demokraɗiyya a Nahiyar Afirka, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya bi sahun jagororin ƙasashen duniya da dubban ƴan ƙasar Gabon wajen ƙaddamar da Brice Clotaire Oligui Nguema a matsayin shugaban ƙasar, ranar Asabar.
Hakan ya biyo bayan nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa da ya yi a ranar 12 ga watan Afrilu, 2025 inda ya doke sauran ƴan takara bakwai a zaɓen.
Nguema ya riƙe shugabancin ƙasar a matsayin riƙon ƙwarya na tsawon watanni ashirin biyo bayan canjin gwamnati da aka samu, lamarin da ya yi sanadin kawo ƙarshen mulkin Shugaba Ali Bongo.
An gudanar da taron ne a filin taro na Stade de I’amitie sino-gabonaise dake Birnin Libreville a ƙasar, inda aka gudanar da faretin sojoji da na wasu hukumomi kamar yadda al’adar ƙasar ta nuna.
A sanarwar da Stanley Nkwocha, Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai na ofishin mataimakin Shugaban ƙasa ya fitar, ya ce Shugaba Nguema ya miƙa godiya ga ƴan ƙasar bisa gagarumin goyon bayan da suka nuna masa.
Ya kuma ci alwashin yin aiki tuƙuru ga harkokin ci-gaban ƙasar gami da inganta rayukan matasa.
Kazalika, ya yi alƙawarin kawo ƙarshen matsalolin rashin tsaro da fashi da suka addabi ƙasar da al’ummarta da dai sauran buƙatun al’umma.
Baya ga Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron, akwai kuma shugabannin wasu ƙasashe da suka haɗa da; Teodoro Obiang Nguema, Equatorial Guinea; Paul Kagame, Rwanda; John Dramani Mahama na Ghana; Faustin-Archange Touadéra na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya; Adama Barrow na The Gambia; Julius Maada Bio, Sierra Leone; Félix Tshisekedi na Jamhuriyar Demokraɗiyyar Congo; Bassirou Diomaye Faye na Senegal da kuma Mahamat Idriss Déby Itno na Chadi.
Sauran sune Denis Sassou Nguesso Jamhuriyar Congo; Ismaïl Omar Guelleh na Djibouti; Umaro Sissoco Embaló, Guinea-Bissau; da Évariste Ndayishimiye na ƙasar Burundi da dai sauransu.
