Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnan Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bayyana cewa babban burin gudanar da bikin Kano Festival of Arts and Culture (KANFEST) shi ne jawo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen waje domin bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin rufe shagulgulan KANFEST na tsawon kwanaki uku, a yayin liyafar karramawa da aka shirya wa mahalarta a Fadar Gwamnatin Jihar Kano da yammacin Litinin.
Gwamna Yusuf ya buƙaci mahalarta daga ƙasashen waje da su kasance jakadun jihar Kano ta hanyar yaɗa dimbin damar saka hannun jari da jihar ke da su a ƙasashensu.
Wannan na ƙunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kano, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Talata.
A cewar sanarwar, Gwamna Yusuf ya jaddada cewa:
“Gwamnatina za ta ci gaba da zuba jari wajen tallafawa fannin fasaha, al’adu da yawon buɗe ido a matsayin muhimman ginshiƙai na haɗin kan al’umma, nishaɗantar da matasa, da bunƙasa tattalin arziki.
Muna da yaƙinin cewa ta hanyar haɗa ilimin gargajiya da na zamani, masu sana’o’inmu za su iya yin gogayya da takwarorinsu a kowane lungu na duniya.”
Gwamnan ya ƙara da cewa, wannan shiri na KANFEST yana cikin manyan tsare-tsaren gwamnatinsa na mayar da al’adu ba kawai abin ajiya ba, har ma masana’antu masu samar da ci gaba da arziki ga al’umma.
Ya kuma nuna godiya ga duk wanda ya ba da gudunmawa wajen tabbatar da nasarar bikin, musamman baƙi daga cikin gida da waje.
A nasa jawabin, wakilin Ma’aikatar Al’adu da Yawon Buɗe Ido ta Tarayya, Dr. Kabiru Ali Masanawa, ya bayyana KANFEST a matsayin sabon tsari da zai taimaka wa Najeriya wajen yaɗa al’adunta da kuma amfani da su wajen jawo jarin ƙasashen waje da bunƙasa yawon buɗe ido.
Shi ma mataimakin gwamnan Jihar Kano, wanda kuma shi ne Shugaban kwamitin Shirya KANFEST, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya jinjinawa Gwamna Yusuf bisa cikakken goyon bayan da ya bayar, wanda ya tabbatar da nasarar shirin.
Ya kuma gode wa Ofishin Jakadancin ƙasar Ruwanda da sauran wakilai daga ƙasashen waje bisa halartar bikin da nufin taya Kano murnar nuna kyawawan al’adunta.
A sakon fatan alheri da ya gabatar, Mai Martaba Sarkin Rano, Alhaji Isa Umaru, ya gode wa Allah Maɗaukakin Sarki bisa bai wa Kano shugaba mai hangen nesa kamar Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda yake aiwatar da manyan ayyuka masu tasiri kai tsaye ga rayuwar talakawa.
Daga cikin abubuwan da suka ɗauki hankalin mahalarta a wajen liyafar akwai bayar da kyaututtuka ga waɗanda suka lashe gasar al’adu da aka gudanar yayin bukukuwan KANFEST na kwanaki uku.
