Wasu sassan Abuja za su ci gaba da kasancewa cikin duhu, inji TCN

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Ƙasa TCN, ya sanar da cewa za a samu tsaiko yayin raba wuta a wasu yankunan birnin tarayya Abuja har na tsawon makonni biyu.

Kakakin kamfanin, Ndidi Mbah ya sanar da haka a wata takarda ranar Litinin.

A cewar TCN, tsaikon zai samu ne sakamakon aikin gina titina da ake yi, wanda zai faru tun daga yau Talata, 28 ga watan Oktoba zuwa Nuwamba 16.

Ya ce, a yayin haka za a rasa wuta a layin Gwagwalada-Kukwaba-Apo mai nauyin kilovolt 132, wato ninki biyu na layin lantarki.

Don haka za a samu ɗaukewar wuta a yankunan Apo, Lokogoma, Guzape, Asokoro, Wuye, Utako, Jabi da Idu Industrial Layout.

Sanarwar ta ƙara da cewa, za a riƙa samar da wuta a yankunan ne a yayin da aka gama aikin kowace rana domin rage musu matsin da hakan ka iya haifar musu.

By Babaji