
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Amurka ƙarƙashin jagorancin Shugaba Donald Trump, ta soke bizar fitaccen marubuci kuma mai lambar yabo ta ‘Nobel’, wato Farfesa Wole Soyinka daga shiga ƙasar.
Rahotanni sun bayyana cewa, an sanar da Soyinka cewa izinin shigar sa ƙasar ya ƙare ne bisa sabuwar dokar da gwamnatin Trump ta sanya wadda ta shafi wasu daga cikin fitattun mutane a duniya.
Farfesa Soyinka, wanda ya shahara wajen kare ƴancin al’umma da ƙoƙarin riƙo da gaskiya, ya daɗe yana da alaƙa da ƙasar Amurka, inda ya yi aiki a da dama daga cikin jami’o’in ƙasar.
Matakin ya janyo cecekuce a tsakanin ƴan Nijeriya da masu fafutukar kare haƙƙin ɗan-adam duba da yadda da dama suka bayyana damuwa akan dalilin da ya sa gwamnatin Amurka ta ɗauki wannan matakin akan ɗaya daga cikin manyan masana da ake alfahari da su a Nahiyar Afirka.
A baya ne Farfesa Soyinka ya ce zai bar Amurka matuƙar Trump ya ci zaɓen ƙasar, inda ya kuma cika alƙawurinsa bayan tabbatar da Trump a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar.
