Me ke hana Kannywood tsallaka iyakokin Arewa?
Daga AISHA ASAS
A cikin shekaru fiye da ashirin da suka gabata, masana’antar finafinan Hausa wadda aka fi sani da Kannywood ta zama wata hanya ta nishaɗi, ilimantarwa da kuma ɗaukaka al’adun Arewa. Finafinai da dama sun ƙayatar da zukatan miliyoyin mutane daga Kano zuwa Katsina, daga Zaria zuwa Zinder. Amma duk da wannan shahara, tambayar da ke ci gaba da yawo tsakanin masana da masu kallo ita ce: “Me ya sa Kannywood ba ta yi amo a duniya ba kamar Nollywood ko Bollywood?”
Shin matsalar tana cikin marubuta ne, ko kuma tsari da kayan aiki? Shin rashin haɗin gwiwa da ƙasashen waje ne ke janyo koma baya, ko kuwa mun gaza fassara finafinanmu zuwa harsunan duniya?
Shafin Nishaɗi na jaridar Manhaja na wannan mako zai yi duba kan matsaloli da kuma amsa tambayoyin da suka jima suna yawo a zukatan masu kallo. Wannan darasi namu zai yi dogaro da bincike mai zurfi, don bayana maku gaskiya game da yadda masana’antar ke tafiya, abin da ya kamata a gyara, da kuma darussan da zamu koya daga sauran finafinan duniya.
1. Tushen matsalar: Daga ina Kannywood ta fara tangal-tangal?
A cewar Farfesa Abdalla Uba Adamu, wanda ya yi fice a fannin nazarin finafinan Hausa, “Masana’antar fim ta Hausa ta fara ne daga ɗabi’ar ƙirƙira cikin gaggawa, ba tare da tsarin ilimi da horo ba.” Wannan kalma tana haskaka yadda fim ke fara fitowa ba da tsari ba, ana ɗaukar bidiyo a gidajen kwana, ana amfani da kyamarorin gida, kuma babu cikakken rubutu ko tsari.
Wannan gaggawa da rashin inganci sun zama al’ada, inda akasari masu fim ke kallon sa kamar kasuwanci kawai, ba wani fasaha ko sana’ar gina ƙwarewa ba. Wannan tasa masana’antar ta rasa amintattun shingaye na masana da matakin ci gaba da take buƙata.
2. ƙalubalen ciki: Rashin horaswa da rage darajar marubuta.
Yawancin finafinan Kannywood suna rasa ƙayatarwar labari da zurfin salo. Dalili kuwa? Rashin darajar da ake bai wa marubuta. Duk da cewa su ke gina tubalin fim, mafi yawan marubutan Kannywood ba sa samun isasshen lada, kuma ana nuna musu ba su da amfani.
A wata hira da Aminiya ta yi da marubucin fim, Naziru Dan Hajiya, ya ce: “Wasu lokuta marubuci kan rubuta fim guda, amma a ƙarshe sai a ƙi saka sunansa ma, balle a biya shi hakkin sa.”
Wannan na nuna cewa, matsalar ba wai rashin ƙwararrun marubuta ba ne, sai dai rashin girmamawa da tsari da ke ƙarfafa su.
3. Finafinan Kudu (Nollywood): Me ya sa suka fi amsuwa?
Nollywood na amfani da fasaha ta zamani, tare da saka jari daga kamfanoni da bankunan Najeriya da ma na ƙetare. Wasu daga cikin fim ɗin su suna samun tallafi daga hukuma kamar Bankin Raya Masana’antu (BOI). Hakanan, sukan fitar da fim ɗin su zuwa duniya ta hanyar Netfliɗ, Showmaɗ da Amazon Prime.
Finafinan Nollywood suna amfani da daraktoci da masu shirya fim da suka samu horo a cikin gida da ƙasashen waje. Misali, fim ɗin ‘The Black Book’ wanda Editi Effiong ya jagoranta a 2023, ya samu nasara sosai a Netfliɗ saboda ingancin sa da shirya shi a tsari na duniya.
4. Tsari da shiri: Bambancin da ke tsakanin finafinanmu da na waje
Finafinan ƙasashen waje suna da matakai na shiri da tsauraran ƙa’idoji kafin fim ya fita. Ana ɗaukar lokaci wajen:
Rubuta labari (Story deɓelopment).
Yin storyboard.
Auditions da casting.
ƙoƙarin samun lasisi da tallafi.
Editing da post-production a manyan cibiyoyi.
A Kannywood kuwa, za ka ga ana yin fim cikin sati ɗaya, babu storyboard, babu amfani da software masu ƙarfi wajen gyara sauti ko hoto. Wannan rashin tsari yana haifar da sauƙin salon aiki da rashin kwarjinin gani.
5. Rashin marubuta masu inganci ko rashin ba su muhimmanci?
Wasu na ganin cewa rashin marubuta masu ƙwarewa ne ke hana fim ɗin Hausa ci gaba. Amma wasu kamar Hafsah Ibrahim, wata mai nazarin finafinan Arewa daga Jami’ar ABU Zaria, sun ce: “Ba rashin marubuta ba ne matsalar, sai dai rashin tsarin da ke gina su, da kuma raina rawar da suke takawa a harkar.”
Kamar yadda aka sani, marubuci ne ginshiƙin fim. Idan ba a ba shi girma ba, to ginin ba zai tsaya da kyau ba. Finafinai kamar ‘ƙueen Amina’ da ‘Lionheart’ sun nuna muhimmancin ingantaccen rubutu.
6. Shirin da ake yi wa fim: Hausa da ƙetare
A finafinan ƙasashen waje, shirin fim yana farawa ne da shekara guda ko fiye kafin a ɗauki hotuna. Ana bincike, ana tuntuɓar masana tarihi, ana duba wuraren da fim zai gudana (location scouting), sannan a fara aikin a hankali.
Misali, fim ɗin ‘Black Panther’ ya ɗauki fiye da shekaru biyu ana shiri kafin fara ɗaukar fim ɗin. Amma a Kannywood, wani lokaci ana iya kawo ‘script’ Litinin, a fara ɗaukar fim Talata, a gama da gyarawa cikin mako guda.
7. Menene matsalar finafinan Hausa?
Matsaloli da dama sun dabaibaye Kannywood:
Rashin saka jari mai ƙarfi.
Gyaran sauti da hoto marar inganci.
Fassarar ra’ayoyi da aka kwaikwayo daga Bollywood ko Nollywood.
Cikakken rashin kayan zamani kamar drone, lighting, da color grading.
Rashin isassun makarantu masu horar da sana’ar fim.
A cewar Ali Nuhu: “Idan har muna son a girmama finafinanmu a duniya, dole mu daina finafinai na yau da gobe, mu koma ginin sana’a da tsarin masana’antu.”
8. Muhimman bayanai game da finafinai: Na Hausa da na duniya
A Hollywood, fim ɗaya na iya kashe dala miliyan 50, yayin da mafi yawan finafinan Hausa ba su kai Naira miliyan biyar ba.
Finafinai na waje na da kariyar haƙƙin mallaka (copyright protection) sosai.
A Najeriya, finafinai da dama sukan fito ba tare da rijista ba.
9. Me ke sa jaruman Hausa shiga matsala bayan sun bar fim?
Yawan jaruman Hausa da ke faɗawa cikin talauci bayan sun daina fim abin damuwa ne da tausayi. Wannan yana faruwa ne saboda:
Rashin kula da haƙƙoƙin fansho.
Rashin sanin yadda ake tsara rayuwa da kuɗin shiga, wato rashin amfani da abinda shahara ta bayar wurin gina wa bayan shahara gida.
Rashin ƙungiyoyi masu kariya da taimakawa jarumai.
Jarumai irinsu Hajiya Balaraba Mohammed, Baba Karƙuzu, da Usman Baba Pategi (Samanja) sun fuskanci ƙalubale na lafiya da kuɗi bayan komawa gefe.
10. Me ya sa jaruman ƙetare ke samun ci gaba bayan dun daina fim?
A ƙetare, akwai tsarin ‘royalties’. Hakanan, yawancin su suna da:
Albashi mai tsoka.
ƙungiyoyin kare haƙƙinsu.
Horo kan yadda za su kula da kuɗinsu.
Wasu kamar Denzel Washington da Morgan Freeman suna amfani da tsofaffin finafinan su wajen samun kuɗi a shekara.
Royalties:
A ƙetare, masana’antar fim ta ci gaba wajen tsarin biyan ‘royalties’ ga jarumai da masu ƙirƙirar finafinai. Idan jarumi ya fito a wani fim, yana ci gaba da samun riba daga cin kasuwar sa, ma’ana, a duk lokacin da aka siyar da fim ɗin, ya Allah a na’urori kamar DɓD ko shahararrun dandamali na intanet, to fa yana da kaso daga riban da za a samu a wannan cinikin, kenan ba a iya biyan kuɗin aiki ne jarumi ya tsaya ba, tamkar saka hannun jari ne, wanda ake ba ka kaso a riban da za a samu. Wannan yana tabbatar da cewa, kowane ɓangare na aikin yana samun haƙƙinsa na kuɗaɗe. Jaruman ƙetare kamar Denzel Washington da Morgan Freeman suna amfana daga wannan tsari, wanda ke taimaka musu wajen kula da rayuwar bayan fim. Wannan tsari yana kuma amfani da su wajen kare haƙƙinsu a cikin masana’antar.
Wani abu game da wannan tsarin kuwa shi ne, yana ƙara ingancin fim, domin idan jarumi ya san cewa, fim ɗin da zai yi yanzu, zai iya samun riba kansa bayan fitarsa, zai yi ƙoƙarin ganin cewa ya yi iya mai yiwa don ganin ya taimaka wurin karɓuwar fim ɗin, don ya san shi ma zai ci daga riban shaharar fim ɗin.
A cikin Kannywood, wannan tsari ba a cika samun sa ba, kuma jarumai suna fuskantar ƙalubale wajen kare haƙƙinsu bayan sun gama aikin fim.
11. Barazanar AI ga masu fim
Wata sabuwar barazana ga masu yin fim ita ce, Artificial Intelligence (AI). Ana iya amfani da AI wajen:
Samar da fuskar jarumi
Rubuta cikakken labari
Gyara bidiyo da murya
Wannan barazana ce ga masu aikin hannu. Amma tana iya zama dama idan aka yi amfani da ita wajen rage kuɗin aiki da inganta sakamako. Duk da cewa masana na ganin ya danganta da ta fuskar da aka kalli wannan cigaban, domin zai iya zama alheri ga harkar. Saidai abinda yake da tabbaci shi ne, zuwan AI a harkar fim zai rage yawan mutanen da ke samun na abinci a ɓangaren.
12. Hanyoyin warware matsalolin da suka yi wa Kannywood dabaibaye:
Gina makarantu na sana’ar fim a Arewa.
ƙarfafa haɗin gwiwa da masu shirya fim na ƙetare.
Gina rumbun finafinai na intanet (streaming platform).
Taimakon gwamnati da lasisi mai inganci.
Gina dokokin kare haƙƙin masu ƙirƙira (copyright laws).
Kamar yadda aka faɗa cewa, fim ba kawai hoto da murya ba ne. Fim falsafa ce kuma rayuwa ce. Idan ba a gina shi da tubalin ilimi da tsarin da ya dace ba, to zai rushe kafin ya kai ginin duniya.
Kammalawa: Daga mafarki zuwa gaskiya:
Finafinan Hausa sun taka rawa matuƙa a tarihin al’adun Arewa, amma akwai gagarumin tazara tsakaninsu da finafinai na ƙetare. Da shiri, tsari, saka jari, da mutunta masu fasaha, Kannywood na da damar kai wa sahun gaba. Wannan ba zai faru ba sai da haɗin gwiwar gwamnati, ƙungiyoyi, masu ilimi da kuma masu kallo.
“Fim ba nishadi kawai ba ne, sana’a ce, rayuwa ce, kuma makoma ce,” inji Farfesa Abdalla Uba Adamu.
