Kano: An ja hankalin ‘yan kasuwa akan kafa ƙananan masana’antu a Bichi

Spread the love

Tsohon Shugaban Jami’an Tsaron Farin Kaya na Kasa, Alhaji Yusuf Magaji ya buƙaci ‘yan Kasuwar Zamani ta Ƙaramar Hukumar Bichi da su cigaba da neman shawarwarin masana tare da haɗa hannu wajen samar da ƙananan masana’antu da haɓaka harkar noman rani.

Yusuf Magaji ya bayyana haka ne a yayin da ƙungiyar ta kai masa ziyara a gidansa dake garin Bichi, ranar Juma’a.

Da yake jawabi Alhaji Yusuf Magaji, ya bayyana matukar farin cikinsa da wannan ziyara, Inda ya bayyana hadin-kan ‘yan kasuwar a matsayin kashin bayan samun nasarar kungiyar.

Ya kuma yi alkawarin taimaka wa ‘yan kasuwar ga dukkan abubuwan da suka sa a gaba, inda daga bisani ya yi musu fatan alheri tare da samun cigaba mai dorewa.

Tun da fari, Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Alhaji Abubakar Mazahim Saleh, ya bayyana jin dadinsu dangane da yadda shugaban ya tarbe su, inda ya bayyana ziyarar a matsayin girmamawa gare shi gami da neman shawarwarinsa, a kan abin da ya shafi kasuwanci da kuma tsaro a Karamar Hukumar Bichi dama Kano ta arewa baki daya.

Kazalika, ‘yan kasuwar sun bayyana Alhaji Yusuf Magaji Bichi, a matsayin shugaba abin koyi wanda tarihin Bichi ba zai taba mantawa da irin gudunmawar da ya bayar ba, musamman wajen daukar matasa aiki a bangarori da dama.

A hannu guda, ƙungiyar ‘yan kasuwar, ta yaba wa Mai ba Gwamna shawara a kan Tsaftar Muhalli, Injiniya Abdullahi Shehu Bichi, sakamakon feshin maganin sauro da aka gudanar a cikin kasuwar hadi da babban asibitin Bichi.

By ukarofi