Kwale-kwale ya kife da sama da mutum 40 a Yobe

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN Damaturu

Jirgin ruwa ƙirar kwale-kwale ya yi hatsari, inda ya kife ɗauke da sama da mutum 40, yan asalin ƙauyen Garbi da Nguru a jihar Yobe, wanda ya taso daga ƙauyen Adiyani ta ƙaramar hukumar Guri ta jihar Jigawa.

Bayanan da wakilinmu ta tattara, hatsarin ya faru ne da misalin 7pm na daren ranar Asabar, wanda ya dauko yan kasuwa mata masu safarar gwaba tare da sauran jama’a, maza da mata.

Malam Musa Ubaliyo Nguru, ya bayyana cewa, jirgin ya kife ne a lokacin da yayi cikar-kwari da mutane sama da 30.

Ya ƙara da cewa, “Yanzu haka an ceto mutane 13 da ran su, tare da gawarwaki 17. An ci gaba da neman sauran mutanen da ba a gani ba.”

Ubaliyo ya ƙara da cewa, waɗanda kwale-kwalen yayi hatsarin dasu maza ne, mata manya da yan mata ne masu zuwa kasuwanci da ziyarar yan uwa a garin Adiyani daga Nguru da Garbi.

Wata majiya a garin ta bayyana cewa kimanin Shekara 40 al’ummar wannan garin basu ga makamancin wannan ibtila’in ba.

A zantawar da wakilinmu ya yi ta wayar tafi-da-gidanka da wani mazaunin kauyen Garbi, Shu’aibu Gambo Abdullahi, ya bayyana cewa, bayanin da suka samu, kimanin mutane 50 ne a cikin kwale-kwalen.

Ya sake tabbatar da cewa, “Hatsarin ya yi sanadiyar mutum 17 tare da ceto mutum 13, sauran kuma an bazama nemansu.”

Ya ce, waɗanda wannan hatsarin ya afka dasu sun ƙunshi maza da mata tare da yara waɗanda suke zirga-zirga daga ƙauyen Garbi da cikin garin Nguru, zuwa Adiyani.

Duk ƙoƙarin jin ta bakin shugaban ƙaramar hukumar Nguru tare da ɗan majalisar jiha, mai wakiltar Nguru, abin ya ci tura, yayin da na kira wayoyinsu ba a daga ba, inda daga bisani na aike musu da saƙon kar-ta-kwana, shima shiru.

By ukarofi