An kama malamin addini bisa zargin hannu a yunƙurin kifar da gwamnatin Tinubu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ana zargin wani fitaccen malamin addinin Muslunci da ke zaune a garin Zariya, Sheikh Sani Khalifa, da hannu a yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Tinubu da wasu sojoji suka yi yunƙuri a kwanakin baya.
Kuma yanzu haka ya shafe kusan kwanaki 23 a tsare a hannun jami’an tsaro.
Majiyoyi da dama da suke da masaniya kan lamarin sun shaida wa wakilinmu cewa, an kama Sheikh Khalifa ne jim kaɗan bayan tasowarsa daga Zariya zuwa Abuja domin neman ba’asin rufe masa asusun bankin da aka yi.

Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin Nijeriya ta musanta yunƙurin kifar da gwamnatin Tinubu da wasu sojoji suka yi a shekarar da ta gabata.
Blueprint Manhaja ta kawo rahotanni daban-daban da kan yadda aka kama wasu manyan sojoji waɗanda ake zargi da ya yunƙurin kifar da gwamnatin Tinubu.
Duk da cewa an fara kama waɗannan sojoji ne a watan Satumba, wasu majiyoyi da suke da masaniya kan lamarin sun shaida wa wakilinmu cewa, fadar shugaban ƙasa ta soke faretin ranar dimokuraɗiyya ta ranar 1 ga watan Oktoba ce domin ɗaukar matakai na kare afkuwar kowacce barazana da ake zato.
Masu yunƙurin juyin mulkin sun shirya kifar da gwamnatin ne a ranar 27 ga watan Oktoba. Sai dai kafin ranar, rahotanni sun tabbatar da cewa an kama jami’an soja sama da 16.
Wannan jarida daga baya ta gano cewa mutanen da suka kitsa juyin mulkin. Wanda ke jagorantar juyin mulkin shi ne birgediya-janar Musa Sadiq da wasu jami’an soja 14 da sojan ruwa guda ɗaya da sojan sama ɗaya.
Sannan an rawaito cewa sojoji sun kutsa gidan tsohon gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva, domin bincike kan zargin juyin mulki. Sai dai ya musanta sa hannu kan wannan yunƙuri.
A cewar iyalan da abokan malam Khalifa, lamarin ya samo asali ne daga rufe asusun bankin malamin ba tare da sanar da shi ba.
Sai dai bai yi nasarar gyara matsalar ba a reshen bankinsa da ke Zariya a yayin da jami’an bankin suka ba shi shawarar zuwa shalkwatar bankin da ke Abuja. Bayan isarsa Abujan ne kuma, a cewar majiyoyin, sai jami’an tsaro suka kama shi tare da tsare shi.
Tsare shin, a cewar wasu da suke da masaniya kan tuhumar da aka yi wa malamin, ana zarginsa ne da karɓar kudi Naira miliyan 2 ta asusun bankinsa daga hannun ɗaya daga cikin waɗanda suka kitsa juyin mulkin.

Mahukunta a Nijeriya sun sha musanta cewa babu yunƙurin kifar da gwamnati wanda hakan ya jefa shakku kan dalilan da suka sa aka kama sojojin.
Iyalan malamin da suka yi magana da wakilinmu a ranar Asabar sun ce, Malam Khalifa ba shi da wata alaƙa da sojojin.
Ya ce, an tura kuɗin ne ba kai tsaye ba domin sai da ya biyo ta hannun wani almajirin malamin wanda shi ne ya san sojan.
“Abin da kawai ya taɓa shiga tsakaninsu shi ne gaisuwa ta waya,” majiyar ta bayyana wadda ta buƙaci a sakaya sunanta saboda iyalan malamin ba su ba da izinin su yi magana ba.
“Daga baya ne sojan ya nemi a ba da lambar asusun malam Khalifa ta hannun wancan almajirin nasa inda ya tura masa kuɗi domin ya yi musu addu’a kamar yadda mutane da dama ke aika wa malamai kuɗi. Amma babu wata magana a tsakaninsu ta siyasa ko wani kasuwanci ko wata yarjejeniya.”
Duk da ba a same shi da laifi ba ana cigaba da tsare shi.
Babban tashin hankalin shi ne yadda majiyar (wani ɗalibin malamin), ya ce, mahukunta sun yarda cewa ba wani wuri da sunan malam Khalifa ya fito da ke nuna zargi kuma an wanke shi.
“Sai dai har yanzu ana cigaba da tsare shi,” ya koka.
A ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Nijeriya , lallai ne a sanar da waɗanda ake zargi da aikata wani abu laifinsu da gurfanar da su a gaban kotu cikin wani lokaci da aka tanada. Hukumomin kare haƙƙin ɗan’adam sun haramta irin wannan tsarewa da ake yi ba tare da sanar da mutum laifinsa ba.
Gwamnatin Nijeriya har yanzu ba ta fitar da wata sanarwa ko bayanin dalilin kama malamin ba.
Mun yi ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar tsaron Nijeriya , Michael Onoja, sai dai bai amsa kiran wayarmu ba har kawo lokacin da muke haɗa wannan rahoto.

By ukarofi