
‘
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya aike da saƙon gargaɗi ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda ya nemi da ya sauka a kujerarsa matuƙar ya nufi ficewa daga jam’iyyar NNPP.
Kwankwaso ya bayyana haka yayin jawabi a wani taron magoya bayansa da masu ruwa da tsaki na NNPP yayin ake tsaka da yaɗa jita-jitar gwamnatin NNPP da ke mulki a jihar na shirin haɗewa da jam’iyyar APC.
Da yake jawabi cikin kakkausan murya, tsohon gwamnan ya ƙalubalen dalilin da ya sa ake neman ɗauke gwamnan daga NNPP, yana mai bayyana hakan a matsayin yunƙurin ƙwace wa NNPP ƙarfinta a matakin zaɓaɓɓun jami’ai.
“Idan kana da gwamnoni 30, mai ya sa sai ka ɗauke gwamnan Jihar Kano? Naka ne”? Tambayar Kwankwaso.
Kwankwaso ya bayyana al’amuran siyasar Kano a matsayin “damuwa” da ke neman caɓewa, inda rikicin ya girgiza mazauna jihar da dama.
Ya ƙara da cewa, ya sha kiran taron masu ruwa da tsaki don ganin an daƙile shirin, wanda ke neman jefa siyasar jihar cikin matsala duba da rashin amfaninsa ga ‘yan jihar.
Kazalika, ya bayyana cewa gwamnatin ta NNPP tana da sauran lokaci na ƙaddamar da kyawawan ayyukan dimukraɗiyya, yana mai cewa haɗin kai tsakanin ‘yan siyasa abu ne mai muhimmanci wajen cimma hakan.
Sanata Kwankwaso ya kuma soki masu kira da a sauya sheƙa waɗanda ya ayyana a matsayin “Gandujiyya”, tafiyar siyasar da ake alaƙanta wa tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.
