
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Juma’a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage shari’ar neman bada belin tsohon Antoni-Janar na ƙasa kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami, ɗansa da kuma matarsa, wato Bashir Asabe.
Alƙalin da ke hukunci akan ƙarar, Mai Shari’a Emeka Nwite ya ayyana ranar 7 ga watan Junairu, 2026 a matsayin lokacin hukuncin akan buƙatar belin mutane ukun.
Alƙali Nwite ya sanya ranar ne bayan lauyoyin ɓangarorin biyu na masu ƙara da kuma na Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, sun gabatar da hujjoji da takardunsu a gaban kotu.
EFCC na zargin Malami, matarsa da ɗansa da aikata laifukan safarar kuɗaɗe da ɓoye asalin kuɗi ta hanyar sayen kadarori da mu’amalar banki a jihohin Abuja, Kano da Kebbi, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Hukumar ta ce, laifukan sun faru ne tsakanin shekarun 2015 zuwa 2025, ciki har da lokacin da Malami ke riƙe da muƙamin minista a gwamnatin marigayi tsohon Shugaban ƙasa Buhari.
Kotun za ta yanke hukunci kan buƙatar belin a ranar da aka ɗage sauraron shari’ar.
Da fari an samu tataɓurza tsakanin jami’an EFCC da na hukumar kula da gidajen gyaran hali (NCoS) akan shirye-shiryen tsaro a lokacin shari’ar, wanda ya samo asali akan wane ɓangare ne zai jagoranci fannin.
