Kano: An kwaɗaitar da al’umma rajistar katin zaɓe a Ƙaramar Hukumar Bichi

Spread the love

An bbuƙaci al’umma a Ƙaramar Hukumar Bichi da su cigaba da fitowa wajen tabbatar da mallakar katin zaɓe ga wanda bai da shi ko yake da matsala domin samun damar kaɗa kuri’arsa a zaɓe mai zuwa na 2027.

A sanarwar da Jami’ar Yada Labaran yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa Manema Labarai, wannan kira ya biyo bayan zaman tattaunawar masu ruwa da tsakin yankin ne a kan tabbatar da adalci ga jama’ar karamar hukumar dangane da zabe mai gabatowa, a ofishin gudanar da al’amuran zabe na yankin.

Kwamitin masu ruwa da tsakin sun cimma fahimtar tantance ababen da ka iya zama nakasu ko aikin baban giwa ga ma’abota kada kuri’a matukar ba su kiyaye ko sun yi la’akari da su ba., duba da abin da Baturen Zaben yankin ya bayyana.

“Wadanda suka yi rijstar onlayin ya kamata su zo ofishin Hukumar Zabe su karasa saboda kada mutum ya zo da kati lokacin zabe yana neman katinsa na zabe babu, sakamakon rashin kammala wa da ya yi. Haka masu zuwa lunguna yi wa yara kyauta; a karshe dole mu gane yara ne kuma bisa ka’ida ba za a yi musu rijistar ba.” Baturen Zaben yankin. Abdur-Rahman Haruna Rafin-Dadi

Bisa haka wannan rukuni na masu kokarin ganin al’umar yankin kowa ya samu ikon yin amfani da damarsa a zaben mai zuwa, suka bijiro da kyawawan shawarwarin saukaka wa jama’ar karamar hukumar hanyoyin cim ma kada kuri’arsu bisa sauke hakkin kowa yadda yakamata, yayin da Wakilin Hakimin Bichi Galadiman Kano ya bayyana gamsuwarsa.

“Na ji dadi da na zo na ji a kan abin da ake, kuma na san cewa wannan aiki gaskiya ba zai samu nasara ba, idsn ba mu ba da gudunmawa ba, tun da mu ne muka fi kowane bangare kusanci da al’uma gaba daya, na ji wadannan tsare- tsare da aka yi kuma na gamsu.” Wakili Abbas Idris Bayero.

Kazalika, a yanzu haka dai kwana 65 ne suka rage na wa’adin gudanar da rijistar zaɓen. Don haka, waɗanda shekarunsu suka cika ƙa’idar rijistar zaɓe a yanzu su je su yi, masu batun sauya akwati, sakamakon canjin wajen zama su hanzarta zuwa gyarawa, waɗanda nasu ya ƙone ko ya koke su ma su yi azamar sabuntawa. Bangaren wadanda suka fara rage aikin yin rijistar zaben a waya ko kafe su hanzarta zuwa dangwalan yatsa da hoto a Hukumar Zaben domin kammalawa su mallaki nasu.

Masu ruwa da tsakin da suka hadu a wajen taron sun hadar da ; Babban Limanin Bichi, Wakilin Hakimin Bichi Galadiman Kano, Kwamadan Hisba, DPO, Hukumar DSS, Hukumar Civil Defense, Wakilan Hukumar Kashe Gobara,, Kansilan Ilimi, Kansilan Tsaftar Ruwa da Muhalli, Hukumar Kiyaye Afkuwar Hadura, Kansilan PRS, Baturen Zaben yankin tare da wasu jami’an hukumar da dai sauransu.

By Babaji