A wani sabon mataki da ya ɗauki hankulan duniya, gwamnatin ƙasar Chana ta kakaɓa harajin kashi 13 cikin 100 kan kayayyakin hana ɗaukar ciki kamar kondon da kwayoyin hana ɗaukar ciki, a wani yunƙuri na daƙile raguwar haihuwa da ke ƙara tsananta a ƙasar.
Sabon tsarin, wanda ya fara aiki tun 1 ga Janairu, ya kawo ƙarshen rangwamen haraji da aka shafe kusan shekaru 30 ana amfani da shi, tun daga shekarar 1994, lokacin da Chana ke tsaurara manufofinta na rage yawan jama’a ta hanyar tsarin haihuwa ɗaya.
Yanzu haka, duk wani magani ko wata hanya ta hana ɗaukar ciki za su fuskanci harajin VAT na yau da kullum, kamar yadda sauran kayayyakin masarufi ke fuskanta a ƙasar.
Bayanan hukuma daga Hukumar ƙididdiga ta ƙasa sun nuna cewa jarirai miliyan 9.5 kacal aka haifa a shekarar 2024, adadin da ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da miliyan 14.7 a 2019. Wannan gagarumar faɗuwa ta sanya gwamnatin Chana cikin damuwa mai tsanani game da makomar ƙarfin aiki da ci gaban tattalin arziki.
A ƙoƙarinta na sauƙaƙa nauyin da ke kan iyalai, gwamnatin ta ɗauki wasu matakai na daban:
an cire haraji kan hidimomin kula da yara, ayyukan haɗa aure da kula da tsofaffi, tare da ware tallafin kula da yara daga harajin samun kudin shiga.
A shekarar da ta gabata, Beijing ta ƙaddamar da tallafin kula da yara na shekara-shekara, tare da umartar jami’o’i su riƙa yaɗa darajar aure, iyali da haihuwa a tsakanin matasa.
Haka kuma, shugabannin ƙasar sun sake jaddada wannan ƙudiri a Taron Tsare-tsaren Tattalin Arziki na ƙasa, inda suka bayyana aniyarsu ta gina kyawawan ɗabi’u na aure da haihuwa domin daidaita ƙaruwar jama’a.
Sai dai masana na ganin waɗannan matakai ba su kai zuciyar matsalar ba. Sun ce tsadar rayuwa, kuɗin kula da yara da ilimi, rashin tabbas a ayyukan yi, da durƙushewar tattalin arziki sun fi tasiri wajen hana matasa yin aure da haihuwa fiye da duk wata doka.
Chana ta shafe shekaru tana aiwatar da tsarin haihuwa ɗaya daga 1980 zuwa 2015, kafin daga bisani ta amince da yara biyu, sannan ta ƙara zuwa uku a 2021. Duk da haka, yawan jama’a ya ci gaba da raguwa, alamar cewa canjin doka kaɗai ba zai iya sauya halin rayuwar al’umma ba.
Shin kakaba haraji kan kayayyakin hana ɗaukar ciki zai iya sa Chana ta samu ƙaruwar haihuwa? Ko kuwa matsalar tattalin arziki ce ke buƙatar waraka?
