Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Mai ba Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, shawara kan harkokin noma, Dakta Tukur ɗayyabu Minjibir, ya bayyana cewa Jihar Kano ce ke kan gaba a Nijeriya wajen ƙirƙire-ƙirƙire da samar da injinan sarrafa kayan amfanin gona na zamani.
Dakta Minjibir ya bayyana hakan ne yayin taron noma da fasahar sarrafa amfanin gona na NAMIS’25, wanda ƙungiyar Connection of Stakeholders in Agricultural Mechanization (CONESAM) ta shirya, ƙarƙashin jagorancin Mista Teddy Eragbai. Taron, wanda Kano ta karɓi baƙuncinsa a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya nuna ƙima da darajar Kano a fannin noma da sarrafa amfanin gona.
Ya ce halartar kamfanoni masu sarrafa abinci, masu ƙirƙire-ƙirƙire, da sauran masu ruwa da tsaki, tare da tattaunawa mai zurfi kan samarwa da sarrafa abinci, ya nuna tsare-tsaren gwamnatin Kano na bunƙasa harkar noma da sauran fannoni na rayuwa.
Dakta Minjibir ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta ɗauki matakai masu muhimmanci wajen samar da taki, iri, da sauran kayan aikin noma, wanda hakan ya taimaka matuƙa wajen samun kaka mai albarka a jihar, duk da ƙalubalen saukar farashin amfanin gona a kasuwa.
Ya bayyana cewa gwamnatin Kano na nazarin tsarin da zai bai wa manoma kariya ta hanyar sayen amfanin gonarsu a farashi mai kyau, domin ƙarfafa su da bunƙasa harkar noma a kakar da ke tafe.
A nasa jawabin, Babban Jami’in Tsare-tsare na CONESAM, Mista Teddy Eragbai, ya ce taron da aka gudanar a Kano ya fi na Benin da Legas armashi da yawan mahalarta. Ya yabawa Gwamnan Kano bisa muhimmancin da ya bai wa taron, musamman ganin yadda manyan kamfanonin sarrafa amfanin gona suka halarta. Shi ma Auwalu Ishak, wakilin kamfanin Dala Foods, ya ce taron ya amfani kamfaninsu matuƙa.
