Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Birgediya Janar Gambo Mai’Adua mai ritaya kuma shugaban kwamitin ƙwato da lalata jabun magunguna da waɗanda aikinsu ya ƙare da kuma miyagun ƙwayoyi na Gwamnatin Jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa, gwamnatin Kano ta haɗa kai da ɗaukacin masu ruwa da tsaki wajen yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Kano domin mai da Kano jiha wacce babu sha ko fatauci mugan ƙwayoyi ko kuma magungunan jabu ko waɗanda aikin sa ya ƙare a jihar domin tsaftacen Kano da alumma ta daga wannan muguwar ɗabi’a mai yi wa al’umma musamman matasa ila a wannan zamani kuma a ko’ina.
Mai’Adu’a ya bayyana hakane a lokacin bikin gangamin kone miyagun ƙwayoyi kwamitin karta kwana da masu ruwa da tsaki su ka kwace daga hannun miyagun mutane masu wannan ɗabi’a a ƙokarinsu na farouto irin wannan miyagun kwayoyi da kuma kama masu hannu a wannan ɗabia mara kyau wanda aka kone miyagun na sama da na billiyan biyu da rabi kamar yadda Maiadua ya bayyana a bikin kone su a ranar Lahadi a dajin kalibawa da ke hanyar ɗanbatta a ranar lahadi da ta gabata.
Haka kuma ya ce ba wannan ne karo na farko ba domin kuwa wannan gwamnatin ta Kano ko a baya ta kama da kuma tattara waɗannan miyagun ƙwayoyi na kimanin billiyan huɗu da aka kone domin kawar da ila da gurɓata rayuwar alumma da waɗannan miyagun ƙwayoyi zasuyi idan ba a ɗau matakin ba don haka gwamnati zata cigaba da haɗa kai da hukumomi irin su NDLEA da hukumar ‘yan sanda, cibil difanse , Karota, Hisbah jamian tsaron sa kai da sauran alumma domin tsarkake Kano daga miyagun ƙwayoyi da a tsarin gwamna Abba.
Tun da farko a jawabin sa gwamnan Kano wanda ya samu wakilcin Dakta Yusuf Kofar Mata kwamishinan maaikatar kimiya da fasaha shugaban kwamitin karta kwana da kawo zaman lafiya ya ce gwamnatin Kano ta Abba kabir Yusuf ta na aiki akan kawar da wannan muguwar ɗabia a tsawan awa 24 ne ba tare da gajiyawa ba kuma duk wani gudunmawa da goyan bay a gwamna ya bawa wannan kwamitin da sauran masu ruwa da tsaki a wannan aiki.
Shi ma a jawabinsa shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi na Kano NDLEA Alhaji Ahmad Abubakar Idris ya ce tsayawa da gwamnatin Kano kan yaƙi da sha da miyagun ƙwayoyi ya sanya jihar Kano yanzu cikin sahun gaba wajen dakile wannan muguwar ɗabia inda kuma ya yabawa gwamna Abba da sauran masu ruwa da tsaki. Shugabani da dama ne sukayi jawabi wajen ƙone miyagun ƙwayoyi a Kano.
