
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Alhamis aka samu labarin wani matashi ɗan shekara 30 mai suna Mutawakkilu Ibrahim a jihar Kano, wanda aka zarge shi da laifin halaka kakansa da kakarsa a sakamakon rikici akan abinci.
Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya faru ne a yankin rukunin gidaje na Ƙofar Dawanau da misalin ƙarfe 9:30 na safe, wanda ya jefa al’umma cikin firgici da alhini.
A wata takarda daga Kakakin Rundunar ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, Muhammad Ɗansokoto mai shekaru 75 da Hadiza Tasidi sune waɗanda aka halaka yayin harin a gidansu.
SP Kiyawa ya ce, wani shaida ya bayyana musu cewa wanda ake zargin ya yi amfani ne da wuƙa ne wajen aikata laifin inda ya raunata mamatan a sassa daban-daban na jikkunansu.
Tuni aka hanzarta kai su Asibitin Murtala Muhammad da ke Kano, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.
Mazauna yankin da iftila’in ya faru sun bayyana abin a matsayin wanda ya same su ba zato ba tsammani.
Shaidu sun bayyana wa manema labarai cewa, dattawan mutane ne da ake girmamawa a unguwar, sannan sun rayu cikin amince tsawon shekaru.
Rundunar ta tabbatar da cewa an kama Ibrahim kuma a yanzu haka yana hannu inda ake gudanar da bincike akansa.
Ta kuma tabbatar al’umma cewa nan ba da jimawa ba za a miƙa shi ga kotu domin ya fuskanci hukuncin shari’a.
