Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi alƙawarin kammala biyan dukkanin ƴan fanshon Jihar Kano haƙƙokin su na garatuti kafin kammala zangon farko na mulkinsa a shekarar 2027.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake ƙaddamar da kaso na biyar na sake biyan ƴan fansho naira miliyan 5000 a ɗakin taro na Coronation da ke gidan gwamnati a ranar Laraba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce fansho da garatuti haƙki ne na ma’aikaci da ya kamata a biya shi da zarar ya kammala wa’adin aikinsa, yace gwamnatinsa tayi kyakkawayn tsari domin tabbatar da kowane ɗan fansho na Jihar kano ya samu haƙƙinsa na garatuti cikin ƙanƙanin lokaci.
Yayi kira ga waɗanda suka samu jinkiri wajen samun kuɗaɗen su da su ƙara hakuri inda yace gwamnati za ta cigaba da biya sannu a hankali har sai ta tababbar kowane ɗan fansho ya samu haƙƙin sa.
Yaja hankalin waɗanda suka samu kuɗaɗen a wannan lokaci da su yi kyakkyawan amfani da su yadda ya dace ta hanyar kafa sana’o’in dogaro da kai domin su tallafi kawunansu da iyalansu.
Ya bayyana damuwarsa bisa yadda gwamnatin da ta gabata tayi watsi da biyan ƴan fansho haƙkoƙinsu wanda hakan ya jefa su cikin wani mawuyacin hali.
A jawabinsa mai martaba Sarkin Rano Amb. Muhammad Isa Umaru ya yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa yadda ya samar da kyakkyawan tsarin biyan ƴan fansho ba tare da an karɓi ko sisin kwabo daga hannunsu ba.
A nasa ɓangaren, shugaban hukumar ƴan fansho ta jiha Alhaji Habu Muhammad Fagge ya godewa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa yadda yake kyautatawa ƴan fansho tun bayan da ya karɓi ragamar shugabancin Jihar kano.
A jabawansu daban-daban mataimakin shugaban ƙungiyar ƴan ƙwadago ta ƙasa Comred Kabiru Ado Minjibir da shugaban ƙungiyar na Jihar Kano Comred Kabiru Inuwa Dakata sun jinjinawa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf bisa yadda yake kulawa da walwala da jin daɗin ma’aikata da ƴan fansho a Jihar kano.
