Gwamnatin Katsina ta naɗa sabbin sakatarorin masarautun Katsina da Daura

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Biyo bayan yi wa dokokin masarautun gargajiyar Jihar Katsina kwaskwarima ta 2025, wadda ta haifar da kafa majalisar sarakuna, hukumar kula da ma’aikatan ƙananan hukumomin Jihar Katsina ta amince da tura sakatarorin masarautun Katsina da Daura da ma’aji da mai bincike.

Bayanin hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi ta Jihar Katsina Malam Jamilu Yakubu ya sanya wa hannu.

Waɗanda aka naɗa su ne Isah Ali a matsayin Sakataren masarautar Katsina da Ibrahim Abubakar a matsayin ma’aji sai Muhammad Salisu Aliyu a matsayin mai binciken kuɗi na cikin gida na masarautar Katsina.

Kazalika, gwamnatin jihar ta amince da naɗin Gazali Muhammad a matsayin sakataren masarautar Daura, sai Musa Yahaya a matsayin ma’aji da kuma Ado Aliyu a matsayin mai binciken kuɗi na cikin gida na masarautar Daura.

By ukarofi