Kano: ‘Yan bindiga tara da ɗan bijilante sun rasu yayin arangama da sojoji a Shanono

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani ba-takashi da aka yi tsakanin ƴan bindiga da sojoji a Bakaji da Unguwar Garma na Goron Dutsen Ƙaramar Hukumar Shanono ya yi sanadiyyar halaka ƴan ta’adda guda tara da ɗan bijilante ɗaya yayin da kuma wani guda ya samu rauni.

Tun da misalin ƙarfe 12 na daren ranar Lahadi ne ƴan bindigar cikin adadi mai yawa ɗauke da muggan makamai suka kai farmaki a yankin.

An gano cewa sojojin sun daƙile shirin nasu ne a lokacin da suka yi arangama da su a wani yanki na shiga garin, inda suka ɗauki tsawon sa’o’i suna ba-takashi a tsakanin su.

Shugaban ƙungiyar tsaron al’umma ta Shanono da Ɓagwai, Alhaji Yahya Bagobiri, ya ce duk da haka sai da ƴan bindigar sun tsere da shanu guda 40 da mutane shida bayan fafatawar.

Ya bayyana cewa, sun kuma bar babura da dama a yayin ja da bayan, wanda ya faru da misalin ƙarfe 6 na safe.

“Saboda sun zo a ɗaruruwa, sai da suka tafi da mutane shida, to amma godiya ga sojoji waɗanda suka mayar da ruwan wuta inda suka kashe tara daga cikinsu sannan suka sanya su tserewa su bar baburansu”, inji shi.

Kazalika, ya kuma yaba wa dakarun sojojin bisa hoɓɓasa da suka yi wajen bai wa yankin kariya domin tabbatar da dakatar da ƴan bindigar daga cimma munanan manufofinsu.

By Babaji