Zamfara: ‘Yan sanda sun daƙile harin ƴan bindiga a Ƙaramar Hukumar Maru

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ƴan sanda a Jihar Zamfara ta ce jami’anta sun yi nasarar daƙile wani mummunan farmakin ƴan bindiga a Garin Maru da ke Ƙaramar Hukumar Marun Jihar Zamfara a safiyar ranar Lahadi.

Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar a wata sanarwa, ya bayyana cewa haɗakar jami’an hukumomin tsaro ne suka gaggauta yin gaba-da-gaba da maharan, lamarin da ya tilasta musu ja da baya bayan samun munanan raunuka na harbin bindigu.

Ya ce, babu wani daga cikin jami’an da ya samu rauni ko yin awon-gaba da wasu daga maharan a yayin fafatawar kasancewar an ƙarfafa jami’ai a yankin da kewayensa tun da jimawa.

A cewarsa, Kwamishinan ƴan sandan jihar, Ibrahim Balarabe Maikaba ya yaba wa ƙwarewar jami’an tare da tabbatar wa al’umma ƙoƙarin rundunar na bai wa rayuka da dukiyoyinsu kariya.

Kwamishinan ya kuma yi kira a gare su da su cigaba da ba jami’an tsaro haɗin kai wajen gudanar ayyukansu a faɗin jihar.

By Babaji