
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Alamu sun bayyana cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano na dab da barin jam’iyyarsa ta NNPP zuwa jam’iyya mai mulki (APC), lamarin da ka iya zama babban haɗin siyasa a jihar.
Majiyoyi da dama a cikin gwamnati da jam’iyyu sun shaida wa jaridar NewsPointNigeria cewa ficewar gwamnan ka iya aukuwa nan ba da jimawa ba domin kauce wa sauya wani hukunci da ka iya bijirowa.
A cewar majiyoyin, tuni Gwamna Abba ya yanke shawarar barin NNPP kuma a shirye yake ya aiwatar da hakan koda kuwa bai samu sanya albarka daga mai gidansa na siyasa na tsawon lokaci kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, wato Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba.
Sun kuma bayyana cewa gwamnan ya yanke shawarar haka ne bayan tattaunawa da neman shawarwarin masu ruwa da tsaki a jihar ciki har da mambobin majalisar dokokin jihar, ciyamomin ƙananan hukumomi da wasu ƴan majalisar tarayya da ke wakiltar yankunan Kano.
Wannan al’amari ya janyo hankalin jama’a musamman yadda a wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen watsa labarai a jiya Lahadi aka ga Daraktan harkokin gwamnatin gwamnan, Abdullahi Ibrahim Rogo yake bayyana goyon bayansa a fili akan komawar Abba APC.
Da yake jawabi a wajen jagororin jam’iyyar a Ƙaramar Hukumar Rogo, Ibrahim Rogo ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki a yankin sun cimma matsayar bin sawon gwamnan duk inda ya koma a fagen siyasa.
Ya bayyana cewa, komawa APC ga gwamnan shi ne abin da ƴan jihar suke so, Nijeriya, da ma shi kansa Kwankwaso, yana mai ƙarawa da cewa jam’iyya mai mulkin ta samar da fagen siyasa mai ƙarfi a faɗin ƙasar.
