Daga DAUDA USMAN a Legas
Al’ummomi mazauna unguwar Mile 12 da ke ƙaramar Hukumar Ikosi–Isheri–Ketu a Jihar Legas sun koka matuƙa kan rushe-rushen gidajensu da wuraren ibada, lamarin da ya jefa ɗaruruwan iyalai cikin mawuyacin hali.
Waɗannan al’ummomi, da suka haɗa da Hausawa, Yarbawa da sauran ƙabilu daban-daban, sun ce rushe-rushen ya afku ba tare da wata sanarwa ko gargaɗi daga hukuma ba.
ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, Alhaji Muktar Jabo, ɗan asalin Jihar Jigawa kuma shugaba a ɓangaren kasuwancin busasshen barkono a kasuwar Mile 12, ya bayyana cewa rushe-rushen ya faru ne a ranar Litinin, 15 ga Disamba, 2025, yayin da suke tsaka da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
Alhaji Muktar ya shaidawa manema labarai a Legas cewa kwatsam suka ga motocin rusau gine-gine suna shigowa unguwar ba tare da wani bayani ko takardar gargaɗi ba.
A cewarsa, a nan take aka fara rushe gidajensa da na makwabtan sa, ciki har da na Hausawa, Yarbawa da sauran ƙabilu.
Ya ƙara da cewa, ba a tsaya a kan gidaje kacai ba, har da masallatai, makarantu Islamiyya da wasu muhimman gine-ginen al’umma an rushe su.
Ya bayyana cewa, zuwa yanzu, akalla gidaje sama da ɗari huɗu ne aka rushe a yankin, lamarin da ya bar mutane da dama ba matsuguni, tare da jefa mata da ƙananan yara cikin halin damuwa da rashin tabbas. A cewarsa, da dama daga cikin waɗanda abin ya shafa ba su taba fuskantar irin wannan iftila’i ba tsawon rayuwarsu.
Alhaji Muktar Jabo ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Legas da ta dubi halin da al’ummar da abin ya shafa ke ciki da idon tausayi, tare da samar da mafita mai ɗorewa, domin rage raɗaɗin wannan bala’i da ya afka musu.
Duk da haka, ya kuma yi tsokaci kan irin ci gaban da kasuwar Mile 12 ke samu a ‘yan shekarun nan.
Ya ce a ƙarƙashin jagorancin babban shugaban kasuwar, Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam, kasuwar na samun kwanciyar hankali, harkokin kasuwanci na tafiya yadda ya kamata, sannan ana ci gaba da ganin ingantattun gine-gine a sassan kasuwar.
A ƙarshe, Alhaji Muktar ya yi addu’ar fatan alheri ga Jihar Legas da Nijeriya baki ɗaya, yana mai fatan samun zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a ƙasa.
