Kano: ‘Yan Shi’ah sun yi zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu, sun yi tir da yaƙar Iran

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dubunnan Musulumi a Kano waɗanda galibinsu ‘yan Shi’ah ne a jiya Juma’a, sun gudanar da zanga-zangar kira ga a bai wa falasdinawa ‘yanci daga mamayar da Isra’ilawa suka yi musu.

Haka kuma, sun yi jima’in rasuwar jagoran addinin Iran, Sayyid Ayatullah Ali Khamenei, tare da yin alla-wadai da hare-haren da Amurka da Isra’ila ke kai wa ƙasar.

An fara zanga-zangar lumanar ne jim-kaɗan bayan sallar Juma’a a yankin Babban Masallacin Fage da ke cikin garin Kano, inda aka ga masu gangamin ɗauke da tutocin Falasɗinu da Iran tare da rera “Free Palestine”, “Death to Isreal”, “Death to America” da kuma “We support Iran”.

Sannan, sun ɗora tutocin Amurka da Isra’ila akan makara masu ɗauke da hotunan Shugaba Donald Trump da Benjamin Netanyahu.

Da yake jawabi ga ‘yan zanga-zangar, Shaikh Sidi Munir Mainasara da ya jagorance su, ya ce an gudanar da taron ne don karrama ranar ‘Quds’ da aka saba yi a Juma’ar ƙarshe ta kowane wata.

A cewarsa, sun wayar da kan jama’a da gabatar da wasu lakcoci a birane da dama a Nijeriya da wasu sassan ƙasar.

By Babaji