An kama kuratan ‘yan sanda biyu da takardun NECO na bogi a Bauchi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Bauchi ta sanar da kama wasu matasa guda biyu da ake zargi da amfani da sakamakon jarabawar NECO ta bogi a wajen neman aikin kurtun ɗan sanda da ake matakin tantancewa a faɗin Nijeriya.

A wata sanarwa da rundunar ta wallafa a Facebook, ta bayyana cewa an kama mutanen biyu ne bayan an gano cewa suna amfani da sakamakon jarabawa iri ɗaya na bogi kuma masu ɗauke da suna iri ɗaya.

Binciken farko ya nuna cewa mutanen biyu suna tafiya tare a dukkan matakan da ake bi wajen gudanar da aikin, lamarin da ya janyo zargi tare da gano cewa takardun sakamakon da suke amfani da su ba sahihai ba ne.

Tuni aka mika waɗanda ake zargin ga jami’an ‘yan sanda na Sashin ‘E’ na rundunar da ke Bauchi domin cigaba da bincike akan lamarin, kamar yadda ta bayyana.

Kazalika, ta ce za ta fitar da ƙarin bayani akan al’amarin da zarar an kammala bincike a kai.

By Babaji