Iran ta kai wa ofishin jakadancin Amurka hari a Bagdaza

Spread the love

Yayin da ake cigaba da gwabzawa a yaƙin Gabas ta tsakiya, wani hari ya auku a harabar ofishin jakadancin Amurka da ke Bagadaza, babban birnin ƙasar Iraƙi.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wasu majiyoyi na cewa an ga hayaƙi na tashi daga ginin jakadancin bayan harin.

Haka kuma, Rahoton Associated Press ya ce makami mai linzami ne ya faɗa kan filin sauka da tashin jirage masu saukar ungulu a harabar ofishin.

Sai dai Agence France-Presse ta ruwaito cewa jirgi marar matuƙi ne ya kai harin.

Rahotanni sun ce harin ya faru ne jim kaɗan bayan kashe wasu mayaƙa masu goyon bayan Iran a wasu hare-hare da aka kai a Bagadaza.

By Babaji