Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya ce a ranar Talata ya wakilci Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf wajen karɓar tawaga daga babban ofishin Jakadancin Birtaniya da ke Najeriya domin tattauna haɗin gwiwar ci gaba tsakanin Kano da Birtaniya.
Tawagar ta samu jagorancin Ms. Cynthia Rowe, shugabar sashen haɗin gwiwar raya ƙasa ta ofishin jakadancin, inda suka kai ziyarar ban girma domin ƙarfafa dangantakar ci gaba da kuma duba ayyukan haɗin gwiwa da ake gudanarwa ƙarƙashin tsarin haɗin gwiwar Birtaniya da Kano.
Kazalika a wani gajeran saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Murtala Garo ya bayyana cewa sun tattauna fannoni daban-daban na haɗin gwiwa da suka haɗa da gyaran tsarin shugabanci, ilimi, lafiya, bunƙasa tattalin arziki, ƙarfafa cibiyoyi da kuma tabbatar da haɗa kowa a harkokin ci gaba.
