Kansilan Guringawa, Muslihu Yusuf ya tallafa wa yara sama da 50 da kuɗin JAMB

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kansilan Guringawa a cikin Ƙaramar Hukumar Kumbotson Jihar Kano ya gabatar wa Babbar Sakatariyar Ilimi ta ƙaramar hukumar Kumbotso da ƙudurin sa na tallafa wa harkar ilimi daga tushe, kana ya gabatar mata da kwamitin da ya kafa na bunƙasa harkar ilimi a mazaɓar sa, wato ‘Guringawa Ward Education Promotion Committee’, inda kwamitin ya ƙunshi ƙwararrun malaman makarantun firamare, sakandare har zuwa jami’a, sannan da masu hannu da shuni da masu unguwanni da sauran jagororin al’umma har 11 a matsayin mambobin kwamitin.

A Alhamis da ta gabata, kwana guda da kai ziyarar kansilan ofishin Sakatariyar ilimi ta ƙaramar hukumar Kumbotson, ya ƙaddamar da yara marayu su 10 da aka samawa gurbin karatu kyauta a makarantun kuɗi da gidauniyar sa ta ‘Tallafi Charity and Development Foundation’, ta ɗauki nauyi.

Bugu da ƙari gidauniyar ta ɗauki nauyin yara 50 da za a ba su horo na musamman kan yadda ake yin jarabawar share fagen shiga jami’a wato JAMB.

A nata jawabin, Hajiya Ramlat Muhammad, wanda ita ce Babbar Sakatariyar ilimi ta karamar hukumar Kumbotso, ta yi matuƙar jin daɗin ta da ƙudirin na Kansilan, inda ta bayyana cewa “Haƙiƙa irin wannan yuƙuri zai taimaka wajen bunƙasar ilimi a gundumar da ma ƙaramar hukumar bakiɗaya”

Ramlat ta yaba wa Kansilan, sannan ta yi alƙawarin ba shi cikakken goyon baya don ganin ya cimma nasara a manufar sa ta tallafa wa marayu da kuma ganin yankin ƙaramar hukumar Kumbotso ya fita daban ta kowace fuska.

Shi kuwa Muslihu Yusuf Aliyu, ya ce irin wannan tallafi ba shi ne farau ba, sannan gidauniyar tasa za ta ci gaba da tallafa wa iya ƙarfin ta don ganin an share wa marayu da mabuƙata hawaye.

“Babban burin mu shi ne mu ga mun faranta wa al’umma rai, musamman marayu da mabuƙata. Sannan indai muka yi kuskure a nusar da mu don mu gyara”, inji shi.