Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya karɓi lambar yabo ta Blueprint Newspapers ta shekarar 2025 kan kula da kuɗaɗen gwamnati da sauye-sauyen harkar noma, yana mai cewa karramawar za ta ƙara wa gwamnatinsa ƙwarin gwiwar yin taka-tsantsan da ci gaba da yin amfani da albarkatun jama’a cikin tsanaki da bunƙasa harkar noma.
Gwamnan Namadi ya bayyana hakan ne a wata wasiƙa mai kwanan watan 5 ga Agusta, 2026, wacce Babban Sakataren Ofishinsa na Musamman, Adamu M. Garun-Gabas, ya sanya wa hannu, a matsayin martani ga wasiƙun da Blueprint Newspapers Limited ta aiko masa na sanar da shi cewa an zaɓe shi domin karɓar lambar yabon.
Namadi ya nuna godiyarsa ga mahukunta da hukumar shirya labarai ta Blueprint Newspapers Limited bisa karrama Gwamnatin Jihar Jigawa da kuma amincewa da ƙoƙarin da take yi wajen inganta kula da kuɗaɗen gwamnati, gaskiya da riƙon amana, da kuma bunƙasa noma mai ɗorewa.
Ya ce lambar yabon ta ƙara ƙarfafa aniyar gwamnatinsa wajen ci gaba da aiwatar da tsare-tsare da shirye-shiryen da za su inganta shugabanci na gari, tallafa wa manoma, ƙara yawan amfanin gona da kuma taimakawa wajen tabbatar da wadatar abinci a Nijeriya.
Gwamnan ya kuma yaba wa Blueprint Newspapers Limited bisa gudunmawar da take bayarwa wajen ci gaban ƙasa ta hanyar aikin jarida mai nagarta da ɗaukar nauyi, tare da ƙoƙarinta na gano da kuma karrama waɗanda suka yi fice wajen gudanar da ayyukan gwamnati a faɗin Nijeriya.
A cikin wasiƙar, Namadi ya bayyana cewa ya karɓi wasiƙun da aka aiko masa a ranakun 3 da 12 ga Mayu, 2026, waɗanda suka sanar da shi cewa an zaɓe shi domin karɓar lambar yabo ta Blueprint Newspapers ta shekarar 2025 kan kula da kuɗaɗen gwamnati da bunƙasa harkar noma.
Ya ce Gwamnatin Jihar Jigawa na matuƙar godiya da wannan karramawa, yana mai bayyana ta a matsayin ƙarin ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da bin manufofin da za su ƙarfafa shugabanci na gari, tabbatar da gaskiya da riƙon amana, da kuma tallafa wa manoma.
Namadi ya ce wannan karramawa za ta ƙara ƙarfafa gwamnatinsa wajen ci gaba da bunƙasa noma ta yadda zai taimaka wajen samar da wadataccen abinci tare da inganta rayuwar manoma da tattalin arzikin jihar.
A ƙarshe, Gwamnan ya sake yaba wa Blueprint Newspapers Limited bisa gudunmawarta ga ci gaban Nijeriya ta hanyar aikin jarida mai nagarta da kuma ci gaba da karrama waɗanda suka nuna ƙwarewa da nagarta wajen gudanar da ayyukan jama’a.
