Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
’Yan takarar shugaban ƙasa da suka haɗa da Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi za su biya kuɗin Naira miliyan 150 kowanne domin kafa allunan tallan kamfen a Jihar Kuros Riba gabanin babban zaɓen 2027.
Hukumar Kula da Allunan Talla da Alamu ta Jihar Kuros Riba (CRISSAA) ce ta bayyana sabon tsarin kuɗin tallan siyasa na waje da za a biya a jihar.
Daraktan-Janar na hukumar, Ubong Sam, ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da Majalisar Shawarar Jam’iyyun Siyasa (IPAC) a Calabar, inda ya yi bayanin sabon tsarin kuɗaɗen.
A cewar hukumar, kuɗin da aka kayyade ga ’yan takarar shugaban ƙasa shi ne Naira miliyan 150, yayin da na gwamna ya kasance Naira miliyan 100, sanata Naira miliyan 50, ɗan takarar Majalisar Wakilai Naira miliyan 25, sannan ɗan takarar Majalisar Dokokin Jiha Naira miliyan 5.
Sam ya ce an tsara kuɗaɗen ne domin tabbatar da adalci da daidaito wajen amfani da wuraren talla a jihar, yana mai cewa kuɗaɗen ba su yi yawa ba idan aka kwatanta da abin da ake karɓa a wasu jihohin makwabta.
Ya ce hukumar za ta tabbatar da cewa tallace-tallacen kamfen ba su ƙunshi kalaman da za su zubar da mutuncin wani mutum ko jam’iyya ba.
Ya kuma yi gargaɗin cewa jam’iyyun da suka karya ƙa’idojin za su iya fuskantar cire allunan kamfen ɗinsu, tara ko gurfanar da su a gaban kwamitin da Hukumar Kula da Talla ta Nijeriya (ARCON) ta kafa.
Sam ya ƙara da cewa babu tarar da ARCON ke kakabawa wadda ta kai ƙasa da Naira miliyan ɗaya.
Hukumar ta kuma umurci dukkan jam’iyyun siyasa da su cire allunan kamfen ɗinsu cikin kwanaki 30 bayan sanar da sakamakon zaɓe.
Sam ya ce idan aka bar allunan bayan wa’adin kwanaki 30, za a ɗauke su a matsayin abin da ke haifar da matsala a muhalli. Ya ƙara da cewa jam’iyyar da ba za ta iya cire nata allunan ba za ta iya bai wa hukumar izinin rubuce domin ta taimaka wajen cire su.
Da yake mayar da martani, Shugaban IPAC na jihar, Injiniya Effiom Edet, ya bayyana sabon tsarin kuɗaɗen a matsayin abin da ya dace, yana mai cewa Naira miliyan 100 ga kuɗin tallan takarar gwamna, Naira miliyan 50 ga sanata, Naira miliyan 25 ga Majalisar Wakilai da Naira miliyan 5 ga Majalisar Dokokin Jiha ba su wuce gona da iri ba.
Ita ma Mai Ba Gwamnan Shawara ta Musamman kan Harkokin Jam’iyyun Siyasa, Ms Nkoyo Otu, ta tabbatar da cewa tsarin zai kasance cikin gaskiya da adalci, ba tare da fifita wata jam’iyya ba.
Sai dai wani jigo na jam’iyyar Action Democratic Party (ADP), Apostle Edet, ya soki sabon tsarin, yana mai cewa kuɗin da aka sanya sun yi tsada matuƙa, kuma hakan na iya hana ƙananan jam’iyyun da ba su da ƙarfin kuɗi yin gogayya da manyan jam’iyyun siyasa.
Labarin ya zo ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa ke ƙara shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027, inda kuɗaɗen tallan kamfen da amfani da wuraren talla ke zama wani muhimmin ɓangare na shirye-shiryen neman ƙuri’a.
