Zaɓen Osun: Disu ya haramta wa Amotekun da sauran rundunonin tsaro shiga aikin tsaro a ranar zaɓe

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sufeto-Janar  na ’Yan Sandan Nijeriya, IGP Olatunji Disu, ya haramta wa Rundunar Tsaron Yammacin Nijeriya, wato Amotekun, da sauran kungiyoyin tsaro na sa-kai da kamfanonin tsaro masu zaman kansu shiga ayyukan tabbatar da tsaron zaben gwamnan Jihar Osun da za a gudanar ranar Asabar.

Haka kuma, IGP Disu ya sake jaddada haramcin amfani da jami’an tsaro dauke da makamai, masu taimaka wa ’yan siyasa da sauran mutanen da ba su da izinin yin hakan wajen raka ’yan siyasa ko manyan baki zuwa rumfunan zabe da cibiyoyin tattara sakamako a ranar zabe.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya, CSP Ani Iniedu, ya sanya wa hannu a madadin IGP a ranar Laraba, rundunar ta ce matakin ya yi daidai da ka’idojin da aka shimfida na tabbatar da tsaron zabe.

“Rundunonin tsaro da gwamnatocin jihohi suka kafa, kungiyoyin tsaro na sa-kai da kamfanonin tsaro masu zaman kansu, duk an haramta musu shiga ayyukan tsaron zabe, bisa ka’idojin Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya na tsaron zabe,” inji sanarwar.

IGP Disu ya kuma gargadi ’yan siyasa, magoya bayansu da kuma duk wani mutum da ke shirin haddasa tashin hankali cewa duk wanda aka kama da hannu wajen satar akwatin zabe, tsoratar da masu kada kuri’a, bangar siyasa ko kuma aikata duk wani laifi da ya shafi zabe, zai fuskanci kamawa da gurfanarwa cikin gaggawa.

A wani mataki na kara karfafa tsaro gabanin zaben, IGP Olatunji Disu ya tura Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, DIG Ishyaku Mohammed, zuwa Jihar Osun domin jagorantar daidaita ayyukan tsaro yayin zaben.

Rundunar ta ce tura DIG Mohammed na daga cikin matakan da aka dauka domin tabbatar da gudanar da zaben cikin lumana, tsaro da kuma sahihanci.

DIG Mohammed zai jagoranci bangaren ’yan sanda na tsarin tsaron zaben tare da aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro karkashin Inter-Agency Consultatiɓe Committee on Election Security (ICCES).

Sanarwar ta ce za a taimaka masa da Mataimakan Sufetocin ’Yan Sanda da Kwamishinonin ’Yan Sanda da aka tura zuwa yankunan Sanatoci uku na jihar domin sa ido kan ayyukan tsaro, karfafa tattara bayanan sirri da kuma tabbatar da daukar matakin gaggawa idan wata barazana ta taso.

Rundunar ’Yan Sandan ta ce ta tanadi isasshen tsaro domin kare masu kada kuri’a, jami’an INEC, kayan zabe, rumfunan zabe, cibiyoyin tattara sakamako, masu sa ido da aka amince da su da kuma ’yan jarida kafin, lokacin da kuma bayan kammala zaben.

Ta kuma tabbatar wa mazauna Jihar Osun, masu kada kuri’a da maziyarta cewa za a samar da isasshen tsaro domin su gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali.

Rundunar ta yi kira ga dukkan wadanda suka cancanci kada kuri’a da su fito su yi amfani da ’yancinsu na zaɓe cikin lumana ba tare da fargaba ba.

Ta kuma sake jaddada kudurinta na gudanar da ayyukanta cikin ƙwarewa, tsaka-tsaki, mutunta ’yancin ɗan Adam da kuma kare tsarin dimokuraɗiyya a yayin zaɓen gwamnan Jihar Osun.

By ukarofi

Leave a Reply