*Yadda za a karrama zaƙaƙuran 2025
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kamfanin Blueprint Newspapers Limited na shirin gudanar da Lakcar Shekara-shekara ta 2025, da kuma bikin bayar da lambobin yabo a Abuja, inda ake sa ran taron zai haɗa manyan jami’an gwamnati, masu tsara manufofi, jami’an diflomasiyya, shugabannin hukumomin tsaro, ’yan majalisa, ’yan kasuwa, malamai da masu ruwa da tsaki daban-daban tare da gabatar da lakcoci.
Za a gudanar da taron ne ranar Talata, 18 ga Agusta, 2026, a Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre da ke Abuja, daga ƙarfe 10:00 na safe.
Babban abin da zai ja hankalin mahalarta taron shi ne jawabin babban baƙo da Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), zai gabatar kan taken “ƙalubalen Tsaro da Ingancin Zaɓen Nijeriya na 2027.”
Sanarwar gayyatar taron ta samu sa hannun Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Blueprint Newspapers Limited, Salisu Umar, a madadin hukumar gudanarwa, mahukunta da ma’aikatan kamfanin.
Blueprint ta bayyana cewa Lakcar ta Shekara-shekara ta zama ɗaya daga cikin manyan dandamalin tattaunawa kan muhimman batutuwan da suka shafi ƙasa, inda masu ruwa da tsaki ke samun damar musayar ra’ayoyi da nazarin matsalolin da ke da tasiri ga makomar Nijeriya.
Baya ga lakcar, taron zai ƙunshi ba da lambobin yabo, inda za a karrama fitattun mutane, hukumomi da ƙungiyoyi da suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban ƙasa.
A cewar masu shirya taron, lambobin yabon za su karrama ƙwarewa da gudunmawar da aka bayar a fannonin hidimar jama’a, bunƙasar tattalin arziki, ƙirƙire-ƙirƙire da shugabanci nagari.
Kamfanin ya ce taron na bana zai samar da wata muhimmiyar dama ta tattaunawa kan ƙalubalen da ke fuskantar Nijeriya, musamman yayin da ƙasar ke ƙara tunkarar babban zaɓen 2027.
Za a kuma mayar da hankali kan alaƙar da ke tsakanin tsaro da gudanar da sahihin zaɓe, tare da duba batutuwan da suka shafi ingancin tsarin zaɓe da makomar dimokuraɗiyyar Nijeriya.
Blueprint ta bayyana cewa halartar manyan jami’an gwamnati, shugabannin tsaro, ’yan majalisa, jami’an diflomasiyya, ’yan kasuwa, masana, ƙungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki zai ƙara wa taron muhimmanci.
