
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tarihin Nijeriya na shiga kowanne gasar Kofin Duniya ta mata tun da aka fara a 1991 ya haɗu da cikas bayan tawaga Super Falcons ta gaza samu damar shiga na 2027.
A daren Alhamis wayewar Juma’a a Casablanca ne Banyana Banyana ta Afirka ta Kudu ta doke Nijeriya da ci 2 da 1, lamarin da ya sa ‘yan Super Falcons ɗin suka gaza samun gurbi a gasar 2027 FIFA Women’s World Cup.
Da fari dai Super Falcons ta yi fatan farfaɗowa daga cire ta da aka yi a zangon wasannin dab da na kusa da na ƙarshe na Kofin ƙasashen Afirka WAFCON a karawarta da Kamaru, amma Afirka ta Kudu ta ƙi ba ta damar haka a wasan ƙalubale na ranar Alhamis.
Mai tsaron gidan Banyana Banyana, Kaylin Swart ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar Afirka ta Kudu akan Nijeriya, wadda a yanzu za ta kara da Balck Queens na ƙasar Ghana.
Wannan rashin nasara da Nijeriya ta samu ya sake jafe ƙasar a halin rashin shiga muhimman gasa a matakin nahiya da duniya baki ɗaya, inda ita ma tawagar Super Eagles ta maza ta gagara shiga gasar Kofin Duniya na 2026 da aka gudanar a Nahiyar Amurka a watannin Yuni da Yuli.
