Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kwamitin Shugaban ƙasa kan Dokar Kafa ’Yan Sandan Jihohi ya tsawaita wa’adin karɓar takardun shawarwari da matsaya daga jama’a da masu ruwa da tsaki kan dokar da ake shirin samarwa.
Kwamitin ya ce an tsawaita wa’adin ne domin bai wa ’yan Nijeriya da sauran masu ruwa da tsaki ƙarin lokaci su shirya tare da gabatar da shawarwari masu zurfi da inganci kan tsarin dokar.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Kwamitin, Femi Gbajabiamila, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa sabon wa’adin gabatar da takardun shawarwari shi ne ƙarfe 5:00 na yamma ranar Juma’a, 21 ga Agusta, 2026.
Gbajabiamila, wanda shi ne Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, ya ce kwamitin na son tabbatar da cewa samar da Dokar ’Yan Sanda ta ƙasa ya samu faɗaɗɗen shawarwari da ra’ayoyin ’yan Nijeriya da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya ce dokar da ake shirin samarwa za ta samar da tsarin gudanarwa, na hukumomi da na kuɗaɗe da ake buƙata domin samar da ingantaccen tsarin aikin ’yan sanda wanda zai dace da sauye-sauyen buƙatun tsaron Nijeriya, tare da tabbatar da ɗaukar alhaki, ƙwarewa da kare haƙƙin ’yan ƙasa.
Ya ƙarfafa gwiwar lauyoyi, ƙungiyoyin fararen hula, ƙwararrun fannin tsaro, gwamnatocin jihohi, ƙungiyoyin ƙwararru, masana da sauran jama’a masu sha’awa da su yi amfani da ƙarin lokacin wajen gabatar da takardunsu.
Gbajabiamila ya ce abubuwan da ake buƙatar tattaunawa a kansu sun haɗa da dorewar samun kuɗaɗen gudanar da aikin ’yan sanda, tsarin umarni da iko, ka’idojin ɗaukar ma’aikata da horar da su, ikon gudanar da ayyuka, haɗin gwiwa tsakanin hukumomi, hanyoyin ɗaukar alhaki da kuma matakan hana katsalandan ko amfani da ’yan sanda ta siyasa.
Ya ce waɗannan batutuwa sun nuna muhimmancin samun cikakkiyar gudunmawar masu ruwa da tsaki wajen samar da tsarin aikin ’yan sanda mai inganci, ɗaukar alhaki, dorewa da kuma dacewa da buƙatun tsaro na al’ummomi a faɗin Tarayyar Nijeriya.
Kwamitin ya kuma nuna godiya ga waɗanda suka riga suka gabatar da shawarwarinsu, tare da ƙarfafa wa sauran masu sha’awar shiga cikin wannan muhimmin tsari da su yi amfani da ƙarin lokacin.
A cewar Gbajabiamila, kwamitin zai gabatar da cikakkiyar daftarin Dokar ’Yan Sanda ta ƙasa wadda za ta kasance a shirye domin aiwatarwa, domin a ci gaba da tsarin duba da kuma aiwatar da ita a majalisa.
Ana buƙatar gabatar da dukkan shawarwari kafin ƙarfe 5:00 na yamma ranar 21 ga Agusta, 2026, ta hanyar shafin intanet na hukuma da aka ware domin karɓar shawarwarin.
