Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya gayyaci Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, zuwa taron shugabannin ƙasashen BRICS, wanda aka shirya gudanarwa a birnin New Delhi na ƙasar Indiya daga ranar 12 zuwa 13 ga Satumba.
Gayyatar na zuwa ne a daidai lokacin da Indiya ke ƙoƙarin ƙara zurfafa dangantakarta da Nijeriya tare da bunƙasa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen ƙasashen Kudancin Duniya, wato Global South.
Babban Kwamishinan Indiya a Nijeriya, Abhishek Singh, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Laraba.
Singh ya ce, ana fatan Shugaba Tinubu zai jagoranci tawaga mai ƙarfi daga Nijeriya zuwa taron.
Ya bayyana cewa, kasancewar Nijeriya a matsayin ƙasar abokiyar hulɗa ta BRICS na da matuƙar muhimmanci saboda ƙarfin tattalin arzikinta da yawan al’ummarta, musamman matsayinta a Afirka.
A cewarsa, Nijeriya, wadda take daga cikin manyan ƙasashen tattalin arziki a Afirka kuma tana cikin ƙasashen da suka fi yawan jama’a a duniya, na da muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa BRICS da sauran ƙasashen Kudancin Duniya.
Babban jami’in diflomasiyyar Indiya ya ce Nijeriya da Indiya na ci gaba da tallafa wa juna a manyan dandamalin ƙasa da ƙasa, ciki har da burinsu na samun kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar ɗinkin Duniya.
Singh ya kuma bayyana cewa kusan Indiyawa 60,000 ne ke zaune a Nijeriya, inda da dama daga cikinsu suka daɗe suna zaune a ƙasar tare da shiga cikin al’adun Nijeriya. Wasu daga cikinsu kuma, a cewarsa, sun fito ne daga ƙarni na biyu da na uku na iyalan Indiyawa da suka zauna a Nijeriya.
Ya ce al’ummar Indiyawa da ke Nijeriya ta zama wata muhimmiyar gada tsakanin ƙasashen biyu, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya, al’adu da kasuwanci.
Haka kuma, ya bayyana cewa cinikayya tsakanin Nijeriya da Indiya a yanzu na daf da kai wa dala biliyan 10, yayin da sama da kamfanonin Indiya 200 ke gudanar da ayyukansu a Nijeriya. A cewarsa, kusan ‘yan Nijeriya 100,000 ne ke aiki a kamfanonin Indiya da ke ƙasar.
Singh ya ce haɗin gwiwar Nijeriya da Indiya na ƙara yaɗuwa zuwa wasu muhimman fannoni da suka haɗa da tsaro da harkokin soja, makamashi, kiwon lafiya, noma da fasahar zamani. Ya bayyana cewa taron shugabannin BRICS da za a gudanar a New Delhi zai ƙara ƙarfafa dangantakar diflomasiyya da tattalin arziki tsakanin Abuja da New Delhi, tare da samar da ƙarin damar haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Kudancin Duniya.
