Ya kamata a yaba wa tawagar tattalin arzikin Tinubu

Spread the love

Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu wasu nasarori a fannin tattalin arziki da suka cancanci a yaba mata, musamman yadda wasu daga cikin sauye-sauyen da ta ɓullo da su suka fara bayyana a kasuwannin hada-hadar hannayen jari, harkokin musayar kuɗaɗen waje da kuma fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba.

Kwanan nan Shugaba Tinubu ya yaba wa tawagar da ke kula da harkokin tattalin arzikin gwamnatinsa bisa hangen nesa, jajircewa da kuma ƙoƙarin da suke yi. Tawagar ta ƙunshi Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Daidaita Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele; Ministan Kasafi da Tsare-tsaren ƙasa, Atiku Bagudu; Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Yemi Cardoso; da Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Nijeriya (NRS), Zacchaeus Adedeji.

A yayin ganawar, shugabannin Hukumar Kasuwar Hannayen Jari ta Nijeriya (NGɗ) sun bayyana wa shugaban ƙasa yadda darajar kasuwar hannayen jarin ƙasar ta ƙaru daga kusan Naira tiriliyan 30 a shekarar 2023 zuwa Naira tiriliyan 160 a yanzu.

Wannan gagarumin ci gaba ne, kuma bai kamata a yi watsi da shi ba.

A zahiri, kasuwar NGɗ ta samu wani gagarumin tashin daraja a bana, inda a rana guda kacal darajar kasuwar ta ƙaru da kusan Naira tiriliyan 5. Haka kuma, a cikin shekarar nan kaɗai, an samu ƙarin darajar da ya wuce Naira tiriliyan 60.

Waɗannan alƙaluma suna nuna cewa akwai wani sauyi da ke faruwa a tsarin tattalin arzikin ƙasar.

ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suka taimaka wajen farfaɗowar tattalin arzikin shi ne gyaran da gwamnati ta yi a harkar musayar kuɗaɗen waje. A baya, masu zuba jari daga ƙasashen waje sun riƙa ficewa daga kasuwar Nijeriya saboda matsalar samun kuɗaɗen waje da kuma wahalar fitar da ribar jarinsu daga ƙasar.

Wannan yanayi ya fara sauyawa.

Sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta aiwatar sun taimaka wajen inganta yanayin kasuwar kuɗaɗen waje, lamarin da ya ƙara ƙwarin gwiwar masu zuba jari na ƙasa da ƙasa su dawo Nijeriya.

Haka kuma, ƙaruwar kuɗaɗen da ake samu daga fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba na daga cikin abubuwan da suka cancanci kulawa. An bayyana cewa fitar da irin waɗannan kayayyaki ta samu gagarumar ƙaruwa a cikin shekarar da ta gabata.

Wannan ba ƙaramin ci gaba ba ne ga tattalin arzikin da ya shafe shekaru yana dogaro da man fetur a matsayin babban tushen kuɗaɗen shiga daga ƙasashen waje.

Abin da ya fi ƙayatarwa shi ne yadda wasu jiragen ruwa da ke shigowa Nijeriya ɗauke da kayayyakin da ake shigowa da su yanzu suke ƙara komawa ƙasashensu ɗauke da kayayyakin Nijeriya da ake fitarwa. Idan aka ɗore a kan wannan hanya, zai taimaka wajen ƙara samun kuɗaɗen waje da kuma rage dogaro da man fetur.

Haka kuma, Matatar Mai ta Dangote ta taka muhimmiyar rawa wajen sauya yanayin kasuwar kuɗaɗen waje. Yayin da Nijeriya a baya take kashe ɗimbin kuɗaɗen waje wajen shigo da man fetur daga ƙasashen waje, fara aiki da matatar ta taimaka wajen rage buƙatar kuɗaɗen waje da ake kashewa wajen shigo da tataccen man fetur.

A ɓangaren samar da kuɗaɗen waje kuwa, fitar da man fetur da matatar ke samarwa na iya ƙara wa ƙasar hanyoyin samun kuɗaɗen waje.

Waɗannan sauye-sauye su ne dalilan da suka sa shugaban ƙasa ke ganin burin Nijeriya na gina tattalin arzikin da ya kai darajar Dala tiriliyan ɗaya ba abu ne da ya wuce ƙarfin ƙasar ba.

Sai dai a nan ne ya kamata mu yi taka-tsantsan.

Girman tattalin arziki ba ya nufin komai idan talakawan ƙasa ba su ji tasirinsa a rayuwarsu ba.

Shugaba Tinubu ya ambaci yawan jama’ar Nijeriya a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da za su taimaka wajen cimma wannan buri. Amma yawan jama’a zai zama kadara ne kawai idan gwamnati ta samar da ilimi, sana’o’i da guraben aikin yi ga matasa da sauran ‘yan ƙasa.

Idan tattalin arziki yana bunƙasa yayin da rashin aikin yi ke ci gaba da karuwa, to akwai hatsarin samun tattalin arzikin da yake girma a takarda amma ba ya sauya rayuwar mafi yawan jama’a.

Saboda haka, babban ƙalubalen da ke gaban gwamnatin tarayya yanzu shi ne mayar da nasarorin tattalin arziki zuwa ayyukan yi, ƙarin albashi, bunkasar masana’antu da ingantacciyar rayuwa ga talakawa.

Babu shakka, sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu sun haifar da muhawara mai zafi. Wasu sun yaba da ƙoƙarin gyara tsarin da suka ce ya daɗe yana buƙatar sauyi, yayin da wasu ke nuna cewa nauyin da ke kan talakawa sakamakon wasu daga cikin matakan ya yi yawa.

Amma duk da haka, abin da ya fi dacewa shi ne gwamnati ta ci gaba da gyaran tattalin arzikin tare da tabbatar da cewa ba a bar talaka a baya ba.

Burin tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya yana da kyau. Amma abin da zai sa wannan buri ya zama abin alfahari shi ne idan miliyoyin ‘yan Nijeriya suka samu aikin yi, ‘yan kasuwa suka samu damar bunƙasa sana’o’insu, masana’antu suka ƙaru, kuma matasa suka samu makoma mai kyau.

Saboda haka, ya kamata a yaba wa tawagar tattalin arzikin Tinubu kan nasarorin da aka samu, amma yabo kada ya zama dalilin daina tambayar gwamnati abin da ya rage a yi.

Gwamnati ta ci gaba da gyare-gyaren da suka fara haifar da sakamako, amma ta kara mayar da hankali kan samar da ayyukan yi da rage raɗaɗin talauci.

Tattalin arziki mai ƙarfi ba wanda alƙƙlumansa kawai suke girma ba ne; tattalin arziki mai ƙarfi shi ne wanda yake ƙara darajar rayuwar mutanen da yake yi wa aiki.

By ukarofi

Leave a Reply