Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su saita irin alkiblar da suke son ƙasar ta bi gabanin babban zaɓen 2027.
Obi ya yi kiran ne ranar Talata yayin da yake gabatar da jawabin fatan alheri a taron tattaunawar dimokuraɗiyya na gidauniyar Goodluck Jonathan na shekarar 2026, da aka gudanar a Bauchi.
Ya ce ya kamata ’yan Nijeriya su fara tambayar kansu irin makomar da suke son gani a ƙasar, tare da haɗa kai wajen sauya abubuwan da suke ganin suna jefa ƙasar cikin koma baya.
ɗan takarar ya jaddada buƙatar ’yan ƙasa su ɗauki matsaya domin tabbatar da cewa zaɓen 2027 ya gudana cikin gaskiya da adalci, tare da samar da sakamakon da masu ruwa da tsaki za su amince da shi.
Obi ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su yi tunani mai zurfi kan makomar ƙasar, tare da neman shugabanni nagari da za su yi aiki bisa gaskiya da riƙon amana.
Obi ya kuma yaba wa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan kan ci gaba da shirya taron tattaunawar dimokuraɗiyya, yana mai cewa irin wannan taro na taimakawa wajen tattauna hanyoyin ƙarfafa dimokuraɗiyya da tabbatar da ’yancin ɓangaren shari’a.
Ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da kada su amincewa shugabanci mara kyau, rashin adalci da amfani da siyasa wajen karkatar da al’amuran ƙasa, yana mai cewa matakan da ake ɗauka a yau za su iya shafar makomar al’ummomi masu zuwa.
