
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An halaka mutane biyu sannan an yi garkuwa da wasu guda shida a Unguwar Aminu da ke Gundumar Kandarawa ta Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina.
Haka kuma, wasu mazauna su huɗu sun samu raunukan harbin bindiga yayin harin, wanda ya auku a ranar Talata da dare, kamar yadda wani rahoton Daily Trust ya bayyana.
Jaridar ta ce waɗanda aka halaka sune Ibrahim Sama’ila da Mashakuru Isa, inda tuni aka yi musu jana’iza a ranar Laraba kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Waɗanda aka sace a ɗaya gefen sun haɗa da maza uku da mata uku, yayin da aka garzaya da sauran huɗun da suka jikkata zuwa asibiti.
Sannan, an ruwaito cewa maharan sun sace wasu dabbobi da fasa shaguna tare da tserewa da wasu tsabar kuɗaɗe, wayoyin hannu da wasu ababe masu daraja.
Mazauna yankin sun shaida wa Daily Trust cewa da fari an hango maharan suna tafiya ta yankin gabashi daga Doma a Ƙaramar Hukumar Faskari kafin daga bisani suka je Unguwar Aminu.
Wannan hari ya ƙara adadin hare-hare akan na baya da ake ƙaddamarwa a ƙauyukan Bakori tun ƙarshen watan Yuli, waɗanda suka yi sanadiyyar kashe-kashe da sacen mutane da dabbobi da ɗaiɗaita mazauna a yankin.
